✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban a kiwon lafiya

Ko akwai hanyoyin da zan bi domin rage illar taba sigari ga kirjina? Abubakar Sadik, Abuja Amsa: Kamfanoni da dama na sayar da sigari sun…

Ko akwai hanyoyin da zan bi domin rage illar taba sigari ga kirjina?

Abubakar Sadik, Abuja

Amsa: Kamfanoni da dama na sayar da sigari sun sha bincike kan hanyoyin da za su bi su rage illarta akalla ga lafiyar huhu, amma duk wadda suka kirkiro sai binciken kimiyya ya zo ya tabbatar cewa fa ba a rabu da Bukar ba. Misali na kwana-kwanan nan shi ne kirkiro tsinken e-cigarette wato wani tsinken lantarki wanda akan sa wa ruwan nicotine zalla ya rika mai da shi hayaki, wai da sunan zai rage illar karan sigari da muka sani. To bincike na nuni da cewa a yanzu dai tsinken yana iya rage illar sigari a kirji, amma ana bukatar tsawon shekaru kafin a sake wani binciken da zai tabbatar da hakan.

Amma abu mafi sauki dai wanda muke yawan nanatawa shi ne mutum ya san yadda zai yi ya rabu da sigari. Akwai ’yan shawarwari da akan ba wanda yake so ya daina, kamar misali:

 

1-Karfin halinka zai iya sa wa ka bari. Haka kawai za ka yi ra’ayin barin sigari kuma ka iya bari. A lokutan azumi an fi samun damar hakan. Wasu idan suka yi irin wannan canjin ra’ayi tashi guda sukan sha wahala saboda sabo da sinadarin nicotine da kwakwalwarsu ta yi.

2-To saboda wannan sabo, wasu sai an yaye su daga kan sinadarin nicotine ta hanyar wasu dabaru ko magunguna, saboda tsaida sinadarin nicotine tashi guda a wasu yakan iya kawo wasu alamu a jiki na rashin lafiya da sa wa kwakwalwa alamun tabin hankali na wani dan lokaci. Akan taimaka wa mai son bari da musayar sinadarin ta hanyar cingam ko alewa ko lika sinadarin a kan fata.

Wadannan sinadarai an rage karfinsu ta yadda ba za su cutar ba sosai. Mutum na sa wa yana ragewa a hankali har a zo a tsayar gaba daya. Idan ana amfani da dayan wadannan, mutum ba zai ji kwadayin sigari ba sosai. Ana iya samu a manyan kyamis-kyamis.

3-Idan wadannan hanyoyi sun gagara kuma mutum yana da ra’ayin daina sha, to akan iya taimaka masa da wasu magunguna masu aiki a kwakwalwa amma sai an je wurin likita ya rubuta.

4-Mai dakinka za ta iya sa wa ka daina shan sigari ko don illar da shan zai mata da ’ya’yanta idan ka kunna a gida, don haka idan ta ji sai ta yi azama ta taya ka.

 

Idan ina ciwon kai yakan zo da habo. Ko hakan na nufin akwai wata matsala?

Daga Umar Ladan, Chiromawa

Amsa: E, kwarai kuwa zai iya nuni da wata matsala a kwakwalwa, musamman ma idan ka taba samun buguwa a ka. Don haka kada ka yi wani jinkiri, ka samu a duba kan nan naka a asibiti, kuma a dauki hotuna. Da fatan za a dace.

 

Me ke kawo wa mutum kafadarsa daya ta fi daya tsayi?

Daga Usman Ibrahim, Gadar Maiwa

Amsa: Wannan matsala na iya faruwa dalilin wani aibi a jikin jariri tun yana cikin mahaifiya, ko kuma wajen haihuwa idan ya kasa fitowa aka zo zakulo shi a ji masa ciwo a kafada, ko kuma idan ya girma ya samu wani ciwo a baya ko a kafada. Ko ma dai wanne ne a cikinsu, likitan kashi da ya gani ya duba, ya yi hoto zai iya gaya maka wanne ne daga cikinsu.

 

Me ke sa jinin wasu mutanen tsinkewa tarara?

Daga Adamu Safiyanu

Amsa: Da ma shi ruwan jini wasu kwayoyin halittu da muke kira clotting factors ne ke rike da shi, suke sa masa dan danko da iya tsayawa idan ya fara kwarara. A cikin hanta ake sarrafa su. To idan wadannan kwayoyin halittu na cikin jini suka kasa samuwa ta sanadiyyar wani ciwo to shi ke nan sai a ce jini ya zama tsinkakke, kamar dai yadda kamu ke tsinkewa. Akwai ciwo musamman mai suna ciwon tsinkewar jini, inda jiki kan kasa sarrafa wadannan sinadarai a cikin jini. Yawanci shi wannan ciwo gadonsa ake yi. Shi ake kira haemophilia. Akwai kuma tsinkewar jini wadda wasu abubuwa da dama kan kawo kamar shan wasu kwayoyin magunguna masu tsinka jini irinsu warfarin da aspirin. Ciwon hanta ma ke nan zai iya sa tsinkewar jini.

Wannan matsala ta bambanta da tsinkewar jini da ake samu idan aka yi hadari ko idan mace ta haihu, domin su wadannan fashewar wata babbar magudanar jini ita take kawo su ba rashin kwayoyin tsaida jini ba.

 

Me ke kawo taurin bayan gida?

Daga Lawal A. Abekuta

Amsa: Taurin bayan gida yawanci rashin cin kayan ganye da na ’ya’yan itatuwa ne suke sa wa, sai kuma rashin motsa jiki. Wani lokaci idan matsalar ta taru ta yi yawa sai fa an je an karbi maganin saukaka matsalar, ko na sha ko na yin dauke, ko kuma ma a yi aikin fitar da shi da ruwan sabulu.

 

Da gaske ne yawan cin taliyar indomi zai iya kawo basir?

Daga Sani Umar

Amsa: E, in dai kai ita kadai ita ce abincinka, ba ka hadawa da ganyaye da ‘ya’yan itatuwa za ka iya samun hakan.

 

Makoshina yakan toshe, kuma ba na iya hadiyar abinci, ga zafi ga wani abu na fitowa a makoshin kamar shinkafa sai warin baki, shi ne nake neman shawara.

Daga Musa M.B

Amsa: Haba Malam Musa, har sai an gaya maka ka nemi magani a asibiti? Makogwaro na ciwo har abinci ba ka iya hadiya. To idan ba a ce ka nemi magani ba da yaya za ka yi, sai ka zauna da ciwon haka? Alamu na cewa kwayoyin cuta sun yi kaka-gida a makoshinka, watakila ma har da diwa tun da ka ce wani farin abu na fita. Sai ka je likita ya leka ya gani ko haka ne, idan akwai diwar a yi aiki a fitar, idan kuma babu a ba ka magunguna kawai. Da fatan za a dace.

 

Ni kuma ina yawan ganin jijiyoyi suna firfito mini a hannu. Shin hakan matsala ce?

Daga I.A., Katsina

Amsa: A’a, ba matsala ba ce, yawan ganin fitowar jijiyoyin jini a hannaye.