Da Dumi Dumi

Amsoshin tambayoyi: Ko me ke kawo saurin tsufa?

Shekaruna 40 amma mutane na yawan gaya mini cewa fuskata ta tsufa. Ko me ke kawo saurin tsufa? Kuma shin me ya kamata na yi?

Amsa: A’a haba Baban Amina, shekaru 40 ai an sha miya, shekaru sun ja sai dai godiya. Wasu mutane da dama musamman a irin kasashenmu ai a shekarunka suke fara tsufa. Ana maganar saurin tsufa ne a wadanda suka fara nuna alamun tsufa a shekarun kasa da 40. Duk da haka dai za mu duba abubuwan da kan kawo saurin tsufa, sai ka duba ka gani wane ne a ciki kake ganin kamar ya jawo naka.

Abubuwa da dama da kan kawo saurin tsufa, wadanda kan sa mutum saurayi haka kawai a ga yana tsofewa. Akwai alamun tsufan da akan gani, wadanda suka hada da furfura da kuma motsewa ko cukuikuyewar fata. Da ma can dai muna girma muna kara tsufa amma idan aka ga tsufan ya yi saurin zuwa to tabbas akwai dalili. Wadannan dalilai kuwa su ne:

 1. Gado: Wasu sukan yi gadon kwayoyin halittu masu sa saurin tsufa misali kamar masu sa saurin furfura. Masu irin wannan haka kawai za a ga da sun fara zama samari sai furfura ta cika musu suma. Amma ban da furfurar kasumba da ta gemu, wadda yawanci yawan aski ne wannan ke kawota
 2. Shan taba sigari: Taba sigari ma na cikin jerin abubuwan da kan sa fata yaushi da saurin tsufa saboda tana hana fata hada wani sinadari mai sa kyan fata na collagen. Gubar cikin sinadaran sigari kuma na busar da fata.
 3. Barasa: Ruwan barasa yakan busar da fata na tsawon lokaci wanda zai sa ta rika yaushi a ga kamar mutum ya fara tsufa
 4. Yawan shan Kofi: Bincike ma ya nuna cewa yawan shan shayin coffee yana daga cikin abubuwa masu bata fata
 5. Rashin cin abinci mai gina jiki: Shi ma rashin cin abinci mai gina jiki yakan hana fata sinadarai irinsu collagen wadanda za su hada fatar ta yi kyau ta yi kwari. Yawan shan suga da abubuwa masu suga suna daga cikin masu sa saurin tsufa, in ji masana.
 6. Yawan shiga rana: Shi ma yawan shiga rana kan kona fata ta yi baki, ya kuma sa sinadaran su ki yin aiki
 7. Rashin samun isasshen barci: Yawan gajiya da rashin hutawa ta hanyar samun isasshen barci ma kan iya bata lafiyar fata. Domin a barci ne jiki da ma fata kan samu su ta da duk wata komada da ta faru da rana. Idan ba a samu isasshen barci ba wannan gyara ba ya yiwuwa
 8. Muhalli: Zama a cikin gurbataccen muhalli ma kan iya bata fata. Misali a ce mutum shi a cikin kura, ko hayaki ko zafi ko yanayi mai kazanta yake aiki, to duka irin wadannan ba za su yi wa fata wani alfanu ba sai dai illa.

To mai ya kamata wanda aka ce yana saurin tsufa ya yi?

Da fari dai sai ka duba ka gani a cikin jerin wadancan abubuwa da aka lissafa wane ne kake ganin ya sa maka yaushi da tsufan fata. Idan ka gano ko mene ne sai ka fara daukar matakai kamar haka:

ADVERTISEMENT
 1. Barin shan taba sigari
 2. Barin shan ruwan barasa
 3. Rage yawan shan suga da kayan zaki wato carbohydrates
 4. Yawan cin abinci mai gina jiki irin wadanda muka sha fada a nan, wato protein
 5. Yawan cin kayan ganyayyaki da na ‘ya’yan itatuwa
 6. Rage yawan shan shayin coffee
 7. Barin shiga rana, sai dai ta hantsi wadda take da amfani domin sarrafa sinadarin bitamin na ajin D. Idan ta kama a shiga rana da tsakar rana mai zafi sai a yi amfani da lema
 8. Yawan zama a muhalli mai tsabta, maras kwatami ko bola ko kura ko wari ko hayaki
 9. Samun isasshen barci na a kalla awa takwas zuwa tara a kowace rana
 10. Za ma ka iya karawa da yawan wanka da sabulai masu gyara fata, da shafa mayuka masu gina fata

Abin da kawai ba za ka iya canzawa ba shi ne idan akwai gadoyin kwayoyin halittu masu sa saurin tsufa a tare da kai. Amma in ban da wannan duk sauran za ka iya wani abu a kai.

Shin cin ganyen alaiyahu daidai yake da cin karkashi a wajen amfani?

Daga Isa Usman Tumu

Amsa: A’a da na duba alfanun kowane ganye a jadawalin sinadaran amfanin da suka kunsa, sai na ga na alaiyahu ya fi na karkashi yawa, domin kusan duka sinadaran bitaman din sun fi yawa a alaiyahu, gami da cewa akwai wani sinadarin bitamin ma na rukunin K wanda alaiyahu yake da shi amma karkashi bai da shi. Shi wannan bitaman mutane ba su cika cinsa sosai ba saboda banda alaiyahu, sauran ganyayen da ake samunsa ba mu da su a kasar Hausa sosai.

Ni tun da na taso ban san wari ba ballantana kamshi, domin hancina ba ya jin ko daya daga cikinsu. Shin hakan matsala ce?

Daga Bilkisu A.A

Amsa: E, matsala ce da muke cewa anosmia. Wasu lokuta a haka akan haifi mutum da shi, a wasu lokuta kuma a yarinta matsalar ke farawa. Idan a haka aka haife ki za a samu a cikin ‘yan uwa wani na da irin matsalar, wato akwai gado. Idan kuma a yarinta kika same ta za a gaya miki cewa watakila kin yi wani ciwo sosai da kike kuruciya wanda ya kwantar, ciwo irinsu sankarau, kyanda da sauransu, duk za su iya sa a daina jin kamshi ko wari. Akwai ma hadari wanda kan sa buguwa a ka ko a hanci, shi ma zai iya sa haka. Mutane masu yawan mura ma kan iya samun wannan matsala.

Idan a haka aka haifi mutum da matsalar, wato matsalar ta gado ce, ko kuma a kuruciya abin ya faru sanadiyar ciwo, kusan babu abin da za a iya yi. Amma idan buguwa ce ko yawan mura, likitan hanci da makoshi zai iya dubawa ya ga ko za a iya taimakawa.

 

Share