✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: Makon fadakarwa kan magungunan kashe kwayoyin cuta

Mako mai zuwa ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware domin fadakarwa a kan magungunan kashe kwayoyin cuta na antibiotics. An ware wannan mako…

Mako mai zuwa ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware domin fadakarwa a kan magungunan kashe kwayoyin cuta na antibiotics. An ware wannan mako ne ganin yadda kwayoyin cuta na bacteria da dama ke bijire wa magunguna, domin a rika wayar da kan al’umma a kan wadannan magunguna don hana su yawan amfani da su barkatai.

Tun zamanin da aka kirkiro su shekaru aru-aru da suka shude ake morar aikin wadannan magunguna. Sun yi kokari matuka wajen kiyaye salwantar rayukan al’ummomi da dama. To amma yadda akan yi amfani da su ba bisa ka’ida ba ya sa mun shiga hadarin za su iya daina aiki, ta hanyar bijire wa cututtuka. To ta yaya wannan bijirewa kan faru?

Kowa ya riga ya san irin yadda amfani da irin wadannan magunguna ya zama ruwan dare a cikin al’ummarmu, ba a mu ’yan Adam ba, har ma a dabbobi. Idan ka dauki misali, wadansu idan suka ji wani rauni a da, maimakon su je asibiti ko kyamis a wanke musu a ba su magunguna, sun gwammace a ce sun sayo kafso na wadannan magungunan sha ko barbadawa a raunin. Wadansu ma har allurar wadannan magunguna suke sayowa su je a yi musu tare da hadin gwiwar wadansu bara-gurbin ma’aikatan lafiya. Ba mu sani ba, a yanzu ko irin wannan mummunar dabi’a ta ragu. Kai a da ko zazzabi mutum ya ji kafin ya je ya nemi maganin zazzabin maleriya sai ya nemi kafso ya afa tukunna. Kai a yanzu ma a abincin dabbobi kamar abincin kaji sai ka ga an barbada wadannan magungunan kashe kwayoyin cuta, wai za su sa kaji saurin girma.

To saboda irin wadannan ne (da kuma abin da muka yi bayani a kansa makon da ya shude, wato matsalar magunguna na jabu) hukumomin lafiya suka damu a kan kada a zo wata rana fa magungunan nan su ki yin aiki akan kwayoyin cuta gaba daya, a dawo irin zamanin da can, lokutan da babu maganin kwayoyin cuta. A wancan lokaci da babu magungunan kashe kwayoyin cuta, cututtuka sukan yi wa al’ummomi kwaf daya, su yi ta barna, inda sukan kashe dubai kafin abin ya lafa.

Yadda za a kiyaye jama’a daga irin wannan tabargaza da wadannan magunguna kuwa shi ne na hana sayar da wadannan magunguna barkatai. Wato ya kamata hukumomi su yi doka cewa kowane kyamis ba zai iya sayar da wannan magani ba idan babu takarda mai sa hannun likita, kamar yadda ake yi wa wasu magunguna masu karfi ko masu sa maye. A kasashe da dama da suka ci gaba a yanzu haka ake yi, wato akwai doka da ta kayyade da iyakance yadda mutane sukan iya sayen wadannan magunguna cikin sauki.

Su kuma al’umma ya kamata su san yadda ake amfani da wadannan magunguna, cewa ba a amfani da su da zarar an ji wani zazzabi, tari ko ciwon kai har sai likita ya duba mutum ya ga ko ya kamata ya sha su. Idan bai kamata ya sha su ba, likita zai ba da wasu kamar na rage zogin zazzabi da sauransu. Idan kuma ya dace ya rubuta, to zai rubuta amma zai kayyade lokacin da za a sha  da yawan da za a sha. Yana da kyau a ce ba a rage ko wuce wannan iyaka ta likita ba. Misali idan ya ba da na kwana biyar kada a kara kwana biyu ko a rage kwana daya, idan ya ba da na mako kada a rage kada a kara. Haka shi ne zai tabbatar da ingancin irin wadannan magunguna a kan kwayoyin cuta.

 

Yaya cikin dan Adam yake ne? Idan aka ci abinci nau’i-nau’i aka sha abubuwa masu ruwa-ruwa daban-daban a wuri daya za su zauna? Kuma idan aka sha magani shi ma nan wurin zai tafi ba wani wuri daban ba?

Daga I.U.J

 

Amsa: A’a ai ina jin mun taba irin wannan bayani, cewa tumbin dan Adam guda daya ne kuma duk abin da aka ci nan yake fara shiga. Kai ko da dabbobi masu tumbi kashi hudu su ma duk nau’in abin da suka ci tumbi daya yake zama kafin daga baya a mayar da su wani sashin na wani tumbin.

 

Da zarar na ci goro sai cikina ya fara ciwo jikina ya fara bari. Ko hakan matsala ce?

Daga Musa Dukke.

 

Amsa: Eh, yana yi wa wadansu haka, kuma yana nufin eh, akwai matsala ke nan goro bai karbe su ba.

 

Ni kuma fatar marainana ce ta yi ja amma ba ciwo. Ko hakan matsala ce?

Daga Sani A.G

 

Amsa: A’a ba matsala in dai zuwa ’yan kwanaki ya baje. Amma idan kullum haka launin wurin yake ya kamata ka je a duba.

 

Ni ma wani lokaci idan na ji fitsari idan na je sai na yi kokari amma ba zai zo ba, ko hakan matsala ce?

Daga Mai tambaya

 

Amsa: Eh, matsala ce amma ba za a iya gane wace iri ba ce saboda abu na farko muhimmi mai tambayar bai yi ba, wato rubuta suna. Rubuta suna yakan bambance mana masu tambaya namiji da mace, domin kowanensu za su iya samun alamu daya amma cututtuka daban. Misali idan kai namiji ne za a iya tunanin kumburin halittar prostate, idan mace ce kuma za a fi fara tunanin shigar kwayoyin cuta mafitsara. Don haka dai sai mutum ya je asibiti an tantance.