Da Dumi Dumi

Amsoshin tambayoyi: Me ake nufi da ‘broad spectrum’ da ‘narrow spectrum antibiotic?’

Shin me ake nufi da jimlolin ‘broad spectrum’ da ‘narrow spectrum antibiotic?’

Daga Daliba Ummi Rigasa

Amsa: Broad spectrum antibiotics na nufin magunguna masu kashe kwayoyin bakteriya da dama ko iri-iri. Narrow spectrum antibiotics na nufin magunguna masu kashe kwayoyin bakteriya iri daya ko biyu.

 

Me ke kawo ciwon kunne?

ADVERTISEMENT

Daga Sa’adu Turunku

Amsa: Shigar kwayoyin cuta cikin kunne shi ya fi kawo ciwon kunne Malam Sa’adu

 

Me ke kawo tari da haki? Wasu lokuta ma har sai in fadi kuma in dade kafin in tashi. Ko mene ne mafita?

Daga Abdullahi Sarsoli, Legas

Amsa: Haba Mallm Abdullahi ana maka kallon wayayye, tunda ga shi a Ikko ma kake, kuma ka ce irin wannan babbar matsala sai ka tambayi mafita? Kai yanzu idan aka tasa ka a gaba za ka rantse lafiya ce wannan? Ka je ka ga likita.

 

Shekaruna 10 ina fama da wata irin mura. An ce sanyi ne na sha magungunan sanyi amma har yanzu ba canji. Shi ne nake neman shawara

Daga Isa Shani

Amsa: Shawara ita ce ka samu babban asibiti a bude maka kati a bangaren likitoci masu duba hanci da makoshi. Su ne za su iya gaya maka wace irin mura ce wannan su kuma ba ka maganin da ya dace.

 

Mahaifiyata ce idan za ta yi alwala da kwanon cin abinci take yi, har shiga bayan-gida take da shi ko akwai hadarin daukar cutuka?

Daga Rayya U. Kano

Amsa: Eh, kwarai za a iya daukar cututtuka daga irin wannan kwano. Amma abin da ya fi ban tsoro wanda ba ki tambaya ba shi ne cewa wannan alama ce ta wani ciwo a kwakwalwa, ko dai sanadiyar tsufa ko wani abu. Mutumin da yake irin wannan halayyar wato samun mutane masu wasu halaye da suka saba al’ada irin wannan yana da kyau a duba lafiyar kwakwalwarsu. Kamar a ce mutum ne yake so ya yi wanka amma sai ya ce ba zai yi da ruwa ba da lemon kwalba zai yi, kin ga ai akwai matsala.

 

Na ji ka yi magana cewa taba sigari na daya daga cikin abubuwan da ke motse fata ya kawo saurin tsufa. Ko tabar wiwi ma na sa haka?

Daga A.W.L

Amsa: Eh, har da ita

 

Game da hutu ko tusa. Mene ne amfaninta da kuma illarta ga wanda ya ji warin?

Daga Sagir U. Funtuwa

Amsa: Amfaninta shi ne cewa mutum yana fitar da iska mai guba da marar guba wadda ciki ba ya bukata. Idan ba a hutu sosai za a rika yawan samun kumburin ciki da gyatsa, wadda ita ma kamar hutu ne amma ta baki. Wato dole dai iska a ciki ta samu hanyar fita, idan ba haka ba ciki ya ki dadi.

Illarta ga wanda ya shaka zai iya zama mai yawa ko kadan. Tusa mai warin gaske tana kunshe da gubar hydrogen sulphide wadda take da wari irin na rubabben kwai da iskar methane mai tsami. To su wadannan wanda ya fitar da su ya samu lafiya ne, bai kamata wani ya shake su ba domin guba ne, duk da cewa dai muna da yadda jikinmu zai yi ya sake fitar da su. Wadansu ma za ka ga idan suka ji warin tusa ai cikinsu kullewa yake, shi ya sa ake so a yi nesa da jama’a idan za a yi hutu.

 

Ina jin wani abu zu, a cinyata na je asibiti an ce gudun jini ne, ko haka ne?

Daga Muhammad Daura

Amsa: An yi gwaji ne ko hoto aka ga gudanar jinin? Idan ba a yi ba ya kamata a samu a je inda za a yi aune-aune da gwaje-gwaje.

 

Cikina da kaina ke ciwo sai na je asibiti aka yi mini awon fitsari da ba-haya da hotuna… ina mafita?

Daga Haruna Gombe

Amsa: To ai bayanin naka bai cika ba, me sakamakon ya nuna?

 

A duk lokacin da na sha sukari ko wani abu mai sukari sai ya kulle mini ciki in yi zawo. Shin wane irin ciwo ke kawo haka?

Daga Dahiru Sunusi, Abuja

Amsa: Akwai wasu nau’in mutane masu samun borin hanji (borin jini na ciki) daga gundarin sinadarin sucrose da ke cikin sukari. Sai dai wannan yakan fara ne tun a yarinta inda ake cewa suna da sucrose intolerance, wanda za a ga yara cikinsu na kumbura idan suka sha abubuwa masu sukarin sucrose. To ba mu sani ba naka ko tun yarintar ya fara. Idan haka ne to maganin shi ne dole ka daina shan sukari, ka maye shi da kayan zaki marasa sinadarin sucrose, ko masu karancin gundarin sucrose din kamar zuma ko dabino ko wani abu makamancinsu tunda su duk sukarin fructose ne ya fi yawa a ciki.

 

Wani abokina ne ya ce mini idan ya sha rake kirjinsa ne yake masa ciwo. Ko akwai matsala ke nan?

Daga Ilyasu Wakili Akuyam

Amsa: Eh, watakila shi ma jikinsa yana kin karbar nau’in gundarin sukarin da ke cikin rake idan ya yi yawa, tunda akwai nau’in sucrose mai yawa a rake

 

Da dare ba na iya cin abinci sai shayi da dabino, ko shin hakan yana da illa ga lafiya?

Daga Habeeb Dangote

Amsa: A’a in dai kana samun cimaka lafiyayya koda akalla sau daya ne a ranar kamar da safe ko da rana, ai ba komai. Wadansu idan suka ci mai nauyi da dare yana ba su matsala, wadansu kuma irina mun fi son mai dan nauyin da dare. Da safe kuma ko ruwan shayi ne zai iya isa, akasin naka.

 

Mene ne ya sa ni ina da kashin kudi?

Daga G.B.A Pandos

Amsa: Kai! Haba dai! Kana da kashin kudi? To ashe mun warke. Idan wasu sun zo a tuna da likita. Akwai mutane da dama wadanda suke haka, ko me suka taba sai alheri. Bambancin halitta ne, Wanda Ya yi halittar ce Yake zabar wanda Ya ga dama Ya ba shi da yawa, Ya kuma ba wani wanda Ya ga dama kadan. Amma a Hausance ne kawai ake cewa mai kashin kudi ba a likitance ba.

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya