✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: Me ke sa idanun wadansu a ga kamar daya babba daya karami?

Me ke sa idanun wadansu a ga kamar daya babba daya karami? Me ke sa haka? Amsa: Akwai abubuwa da dama, tun daga buguwa ta…

Me ke sa idanun wadansu a ga kamar daya babba daya karami? Me ke sa haka?

Amsa: Akwai abubuwa da dama, tun daga buguwa ta hadari har zuwa tsiyayewar ido, zuwa wani ciwo na daban kamar bugun jini a kwakwalwa ko shigar wasu kwayoyin cututtuka ido ko matsalar wasu jijiyoyin ido, ko fatun ido, har zuwa ma yawan murtsuka fatar idanun idan suna kaikayi, duk za su iya sa wannan. Sai kuma tsufa. Tsufa ma shi ne babban abin da kan sa haka, ka ga ido daya babba, daya karami, domin za ka iya ganin tsofaffi da dama da wannan matsala ba tare da wani ciwo ba. Wani lokaci kuma ka ga daya kamar ya yi sama, daya ya yi kasa. Wadansu kuma ba ciwo ba komai haka aka halicce su, wato akwai bambancin halitta.

Idan kuma kana nufin kankantar kwayar ido ce, to ita ma wannan wadansu haka aka halicce su da bambancin girman kwayar ido wadansu kuma sai da aka haife su suka samu wasu cututtuka suka maida musu da kwayar idon haka. Idan aka ga mutum lafiyayye  wanda da ba ya da matsalar, idonsa daya ya fi daya, ya kamata a nusar da shi, saboda ba kowa yake ankara da irin wannan matsala ba. Idan ma ta kama ya je ya ga likitan ido ne hakan shi ya fi.

Shekara 15 da suka wuce kare ya taba cizona amma wurin ya warke yanzu. Sai daga baya ne nake ji ana cewa akwai allurar da ake wa duk wanda kare ya ciza. To ko yanzu za a iya mini ita?

Daga Kabir Sani

Amsa: A’a ba komai tunda dai abin ya wuce. Allurar da ake yi da ma kiyaye ciwon haushin kare take, wanda kan zo ’yan kwanaki bayan cizon. To amma tunda lokaci mai tsawo ya wuce haka ba amfani a yi maka yanzu.

Me ke sa idan na yi musabaha da mutane suke cewa jikina da zafi, alhali kuma ba na jin zafin?

Daga Rabi’u S. Kebbi

Amsa: Watakila ba komai in dai kai garau kake jinka, domin akwai mutanen da suke irin ka da dama, su kullum jikinsu da dumi, duk da dai an fi samun irin wannan a mata. Wasu sinadaran hormones ne ke sa haka.

Me ke kawo kuraje masu kaikayi fesowa a jikin mutum bayan shan wani magani ko allura?

Daga Aliyu Bala

Amsa: Borin jini ne, wato alamar jikinsu ba ya son wannan magani ke nan ko allura, abin da muke kira adberse drug reaction. Duk wanda ya sha wani magani ko aka yi masa allura ta sa masa haka, to ya rike sunan maganin ko allurar kada a sake ba shi domin alamar ba ta karbe shi ba ke nan.

Me ke kawo yawan habo a lokacin sanyi?

Daga Junaidu Sada

Amsa: Bushewar yanayi a lokacin sanyinmu shi ke kawo yawan habo. Ka san akwai magudanan jini kanana a saman hanci wadanda lokacin bazara suke bushewa har su iya fashewa, lokutan damina kuma su yi danshi ta yadda zai yi wahala su fashe. Amma ka sani cewa a irin kasashenmu na Kudancin duniya akan samu haka. A kasashen Arewacin duniya, inda ake ruwan sama sosai lokacin sanyi su ba su cika samu ba, sai lokacin zafi, shi ne lokacin da ba ruwa a can, suke samun irin wannan nau’i na habo.

Ina samun ciwon baya ne sai na je kyamis aka ba ni magunguna. To amma magungunan suna sa mini ciwon kirji daga kasa. Mece ce shawara?

Daga Haruna Umar Hadeja

Amsa: Shawara ita ce ka bar magungunan kyamis ka je asibiti a binciki me ke yi maka ciwo a gadon bayan tukuna kafin a yi magani.

Mene ne amfanin daci da bauri ko akasin haka ga jikin dan Adam?

Daga Muhammad Auwal, Abuja

Amsa: Duk da cewa yawancin magunguna har da na nasara suna da bauri ko daci, mu dai a likitance sai an san mene ne ainihin sinadaran amfani da ke cikin abu kafin a ce zai iya magani ko a’a. Ban da sanin ainihin sinadaran amfani, sai kuma an dubi gubar da ke ciki, idan akwai, a gani ko za ta iya illa ga lafiya. Akan auna a kan dabbobi ma idan ta kama kafin a gwada a mutane. Duk wadannan matakai sai an dauke su an tabbatar ba matsala kafin ka ga maganin nasara ya shigo kasuwa. Sa’annan domin an san wasu magungunan za su iya sa amai saboda daci, yawancin masu dacin za ka ga an lullube su da kwanso na kafso domin a ji dadin hadiya.

To mu illar irin magungunanmu na gida, sai ka ji ana cewa daci da bauri kaza zai yi maganin kaza, amma shi mai maganin a mafi yawan lokuta koda ya san sinadaran maganin, bai san yawan gubar da ke cikin wannan bauri ko daci ba, ballantana a fara tunanin hanyoyin rufe maganin a kwanso. Illar wannan daci da bauri kuwa a hanta da koda yawanci take karewa, ka ji an ce ai hanta ko koda ta tabu saboda yawan shan daci da bauri wanda ba a tantance ba.

Tambaya nake game da ciwon hanta, amma ba ta yi tsanani ba. To likita ya ba ni wasu bitaman shi ne nake so in san ko akwai wani maganin da zan kara don warkewa da wuri.

Daga Safiyanu Mu’azu

Amsa: A’a ai da ka yi bayanin ko wane irin ciwon hanta ne ke damunka da amsar taka ta fito kai-tsaye. Yawanci dai cututtukan hanta ba su da maganin warkarwa sai dai mai rage kaifin ciwon.

Ina yawan samun wasi-wasi da surutai da ’yan sake-saken zuci. Shin hakan na nufin akwai matsala?

Daga Ashiru A. Katsina

Amsa: Eh, kwarai da alamun akwai matsala. Ka samu likitan kwakwalwa ya dan duba ka ya tabbatar ko hakan ne ko kuma a’a.