✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: Watan yaki da cutar Sankarar Mama

Wannan wata na Oktoba a duk shekara hukumomin lafiya na duniya suka ware domin tunatarwa a kan hanyoyin kariya daga sankarar mama wadanda za a…

Wannan wata na Oktoba a duk shekara hukumomin lafiya na duniya suka ware domin tunatarwa a kan hanyoyin kariya daga sankarar mama wadanda za a kara maimaitawa yau domin mata wadanda ba su taba karanta rubutun ba.

  1. Babbar hanyar kare kai daga kamuwa daga kansar mama ita ce ta yawan shayarwa. Wato masana sun yi amanna cewa shayar da yaro akalla tsawon shekara biyu yana iya kare mace daga kansar mama. Haka kuma yawan yaran da matar ta shayar, yawan kariyar ke nan.
  2. Sai kuma rage kiba. Masana sun tabbatar da cewa mace mai kiba tana cikin hadarin kamuwa da ciwon sankarar mama musamman idan wata a danginta ta taba yin ciwon. Don haka sai a rage maiko a abinci a rika kuma yawan motsa jiki
  3. Sai rage shan kwayoyin nan na ba da tazarar iyali wato OCP ko pills. Domin su ma wadannan kwayoyi an tabbatar suna iya jawo wannan ciwo na sankarar mama. Idan da hali ke nan gwara a bi wasu hanyoyin dabarun tsara iyali ba ta wadannan kwayoyi ba.
  4. Duk matar da ta kai akalla shekara arba’in yana da kyau ta koyi yadda ake duba mama. Wannan wata hanya ce da mace za ta bi ita kadai a dakinta ko ita da mai gidanta domin duba mamanta a mudubi ko za ta ga wani sabon abu a jiki kamar kari ko tattarewar fata. Yadda ake yi kuwa shi ne: mace ta tube ta sa katon mudubi gaba ta dora hannayenta kan kugunta, ta duba ta ga ko akwai wancan yanayin da aka fada. Bayan ta gama sai ta juya ta gefe ta sake yin haka (wato ta duba gefen dama da hagu). Daga nan sai ta sake kallon mudubin, ta sa hannunta na hagu a bangaren dama ta fara latsawa daga gefe zuwa ciki, daga kasa zuwa sama, har karkashin hammata, ta ji ko za ta ji wani kullutu ko kari. Sai ta sake dawowa kan maman ta matso shi ko za ta ga wani ruwa ya fito (idan ba shayarwa take ba ke nan). Idan ta gama sai ta je bangaren hagu ta yi kamar yadda ta yi a dama. Idan babu komai shi ke nan ta gama sai bayan akalla wata shida kafin ta sake. Amma idan ta ji wani kullutu ko tattarar fata ko wani sabon canji ko ta matso wani launin ruwa, to dole sai ta je asibiti an kara bincikawa. Kada a ji tsoro domin a mafi yawan lokuta idan aka ji kullutu ko kurji, ba kansa ba ce kari ne wanda da an yi ’yar tiyata an cire shi shi ke nan.

Wasu shaci-fadi game da kansar mama su ne wai man shafawa na hammata (roll-on) ko saka matsattsiyar rigar mama na iya kawo ciwon daji. Wannan ba gaskiya a ciki.