✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyin da suka shafi abinci

Wai shin babu Ranar Abinci ta Duniya ce? Na ga akwai ranar kowace cuta amma ban ji ana kiran ranar abinci ba, ganin cewa abinci…

Wai shin babu Ranar Abinci ta Duniya ce? Na ga akwai ranar kowace cuta amma ban ji ana kiran ranar abinci ba, ganin cewa abinci ne ginshikin lafiya.

Amsa: Akwai mana Malam Muhammadu, akwai Ranar Abinci ta Duniya mana, kamar a ce ranar ciyarwa ta duniya. A Turance ita ce ranar da ake kira World Food Day. Abin da ya sa ka ji ba a cika kiranta a wannan shafi na lafiya ba, shi ne cewa ai mu a addinance da ma a al’adance kullum rana ce ta ciyarwa, ba sai an ware mana wata rana ba a kullum mutanenmu suna ciyar da almajirai da sauran mabukata, ballantana a zo maganar ranakun ciyarwar azumi da na Zakkar Fid-da-Kai. Wadannan tun kafinTurawa su waye muna da su.

Sai dai kawai abin takaicin shi ne har yanzu a kasashen da suka fi yawan Musulmi aka fi samun yunwa da tashe-tashen hankula masu sabbaba yunwar. Wannan ne ya sa su mutanen Yamma suka samu kafa ta sanya irin wadannan ranaku, inda kusan za a ga domin kasashe matalauta ake tsara wadannan ranaku.

A gidanmu ana yawan cin dafaffiyar gyada da dare. Shin hakan na da amfani ne ga lafiyar jiki ko a’a?

Daga H. M. Jos

Amsa: A’a ba wata matsala in dai ba kulle miki ciki take ba. Domin wadansu takan kulle musu ciki kamar yadda wake kan kulle wa wadansu ciki, tunda dukkansu kusan dangin juna ne. abinci ce mai kyau da lafiya, nau’in mai gina-jiki, sai dai yana da kyau a dan kara da mai ba da kuzari kamar dafaffiyar masara a hada da mai kara bitaman kamar dafaffen alayyahu ko yakuwa a hada. A yanzu kuma da ake bikin Sallah idan an yi suya sai a dan kara. Daidai ke nan.

Abinci idan babu barkono a ciki sam ba na jin dadinsa. Shin yawan cin barkono ba zai iya jawo mini illa ba?

Daga Adam M.

Amsa: Eh, cin barkono da yawa wato ka rika zabga shi har idanu da hanci su rika ruwa zai iya yi wa bangon cikinka illa ya sa olsa. Amma idan saisa-saisa kake sa shi, kuma ba ka taba jin ya sa maka ciwon kirji ko zafin kirji ba, to ba matsala.

Mene ne amfanin sinadarin bitamin D a jikin mutum?

Daga A.B.A, Abuja

Amsa: Sinadarin bitaman D shi ne sinadarin da ke taimaka wa sinadarin calcium wajen aikin kara karfin kashi da hakora a jikin dan Adam.

An ba ni awon ciwon suga na awa biyu bayan cin abinci. To da na ci abinci sai na sha lemon zaki. Shin ko wannan zai iya shafar sakamakon?

Daga Mai-Neman Bayani

Amsa: A’a za ka iya cin komai in dai kana so, ana so ne ka ci abinci kamar yadda ka saba, wato da ma idan kana shan lemon zaki bayan cin abincinka za ka iya sha. Shi ma wannan gwaji na daya daga cikin hanyoyin da akan gane mai ciwon suga. Yadda ainihin gwajin yake shi ne, da fari za a ce kada ka ci abinci na tsawon wani lokaci, akalla awa 8, sa’annan sai ka ci abincin da kake so kamar karin kumallo, wanda dole ya hada da sinadarin carbohydrate, wato kamar burodi, ko dankali ko dumamen tuwo da sauransu. Bayan ka gama ka zauna ka huta, bayan awa biyu ka je a yi maka. Ko takawa ba a so ka yi don haka zai iya shafar sakamakon, don haka kada ka koma a kafa, sai dai a abin hawa, ko ma ka ci abincin a cikin asibitin.

Kana gama cin abincin nan sugarka ke hawa, amma a ka’ida cikin awa biyun nan ya kamata a ce sugarka ta dawo daidai. Don haka daidai wannan lokaci idan aka auna aka ga ta dawo daidai to shi ke nan, idan kuma ta hau to akwai ciwon suga.

Idan na yi tafiya mai dan nisa sai cinyoyina su kama ciwo. Ko hakan na nufin akwai wata matsala ce?

Daga Murtala Ahmed Kwalli

Amsa: A’a ba wata matsala rashin sabo ne, idan ka saba za su ware su daina ciwo.

Da gaske ne ciwon amosanin ido ba ya warkewa? Wadanne hanyoyi zan bi domin in samu sauki?

Daga Aliyu N.

Amsa: A’a, a yanzu a wannan zamani cututtukan ido kadan ne ba a iya warkar da su, kuma yawancinsu wadanda ba a iya warkarwar na makanta ne. Don haka kai ma taka matsalar idan ka kai wa likitan ido ya gani zai iya sama maka mafita. Ita ce hanyar da za ka bi.

Wani lokaci sai in farka in ji gefen wuyana na mini ciwo gefe guda, da an jima sai ya haura kai. Shin hakan matsala ce?

Daga Abubakar Baba, Kano

Amsa: Idan wuya ne kawai kusan ba matsala, musamman idan ka kwanta ba daidai ba ko ba yadda ka saba ba, kamar idan ka saba kwana a katifa sai ka canja zuwa tabarma, ko idan ka saba kwana ba matashi amma sai ka sa matashi, ko kuwa a’a ka saba kwana da matashin amma ranar ba ka sa ba, to idan a irin wannan hali ne ba matsala sagewar wuya ne kawai, wanda zai tafi bayan kwana biyu. Amma in dai ka ce ba a irin wannan yanayi ba ne, kuma yana hadawa da ciwon kai to sai ka je an binciki dalili.

Shin da gaske rashin tsabtar jiki ne ke kawo maruru?

Daga: Yana Garba Gashuwa da Zainab Yahaya Nguru

Amsa: Eh, kuma a’a. Mun taba dogon bayani a kan maruru, ya kamata ku duba ko ta kafar yanar gizo ta wannan mujalla ko a lafiyarmu.com. Abin da ya sa aka ce eh shi ne masu kazanta wadanda ba sa wanka a-kai-a-kai za su iya samu. Abin da kuma ya sa aka ce a’a, masu raunin garkuwar jiki kamar masu ciwon suga ko sida, komai yawan wankansu su ma suna yawan samu, saboda raunin garkuwar jiki. Da ma kwayar cuta ce akan fatar kowa ke haddasa ciwon. Idan kana yawan wanka kana wanke ta ta ragu ba za ta iya sa ciwo ba, amma idan ba a yawan wanka sai ta taru ta shiga karkashin fata ta kawo diwa Su kuma a wadanda garkuwarsu ta yi rauni ko ba su taru da yawa ba saboda rashin kwayoyin yaki da ita, za ta iya sa musu. Wato bambancin a mai tsabta shi ne sai sun taru sun ci karfin garkuwar jiki.