Da Dumi Dumi

Amsoshin tambayoyin da suka shafi abinci

Amsoshin tambayoyin
Amsoshin tambayoyin

Shin me ke kawo yawan ciwon jiki da gabobi ba tare da mutum ya buge ba?

Daga Muhammad Musa Dagora

Amsa: Akwai abubuwa da dama. Yawace-yawace da buga-bugar yau da kullum ma kadai ai za su iya sa ciwon jiki da gabobi. Kai ko zama kake wuri guda ba ka motsawa domin iko ko gata, jikinka zai iya tambayarka. Ke nan yawan zirga-zirga da yawan zama wuri daya duk ba su da alfanu. Dole a samu wani yanayi na tsaka-tsaki a cikinsu. Kamar motsa jikin mintoci 30 a ranaku hudu ko biyar na mako, wato ba ma kullum ba. Ban da wadannan, wadanda ba ciwo ba ne, akwai kuma abubuwa na ciwo masu kawo ciwon jiki da gabobi, wato kusan kowane irin ciwo ma fa zai iya kawo wadannan alamu. Don haka dai ciwo ne da ke da wuya a gane idan ba duba mutum aka yi a asibiti ba.

Me ke kawo zogi ne a kafa? Kuma ya za a yi a rabu da shi?

Daga Zubi I. Jos

ADVERTISEMENT

Amsa: Akwai abubuwa da dama masu sa irin wannan matsala Malam Zubi. Da kana bin mu sosai a wannan shafi da tuni ka san su. Bari mu dan yi maka matashiya; akwai ciwon kafa na ciwon sanyin kashi da ake kira rheumatism akwai kuma na sinadarai irin su uric acid, ciwon da ake kira gout, akwai kuma zogin kafa wanda na mutane masu nauyi ne sosai, wato shi ba wasu sinadarai ba ne ko ciwo, a’a nauyin mutum ne idan ya yi yawa kawai sai kafarsa ta kasa daukarsa, tafin kafa ya kasance kullum zogi. Akwai sauran ire-iren abubuwa masu sa ciwon kafa wadanda sai an yi maka tambayoyi da gwaje-gwaje a asibiti za a iya ganowa, misali kamar idan ka taba yin kwallo ko wani wasa na tsawon shekaru, shi ma yana taba lafiyar kafafu.

Mene ne ainihin fa’idar yin ruwan dumi idan mutum ya buge ko ya samu matsalar ciwon jiki. Za ka ji ana cewa sai ya yi ruwan dumi?

Daga Musa Kasim, Daura

Amsa: Eh, akan ce a yi ruwan dumi idan jikin mutum na ciwo, kamar idan ciwon jikin na gajiya ne, ko idan ya buge wurin ya kumbura. Amma idan sabuwar buguwa ce, a ilimance maimakon zafi an fi son sanyi, wato maimakon a yi gashi da ruwan dumi, an fi so a yi tausa da kankara. Domin an gano kankara ta fi ruwan dumi sanyaya wurin da yake ciwo, ta kuma fi sakin kumburi fiye da ruwan dumi.

Za ka ga a filin kwallo wani idan ya buge za a zo da wani abu a mayani ana goga masa a wurin, to kankara ce. An sa ta a mayani ne saboda kada sanyin ya damu mai aikin gogawar. Amma idan kumburin da ciwon gabobin ya dan kwana biyu za a iya yin ruwan dumin. Wannan fa idan aka je asibiti aka duba aka yi hotuna da gwaje-gwaje aka ce ba komai ke nan.

Ni kuma sai ina tafiya nake ganin wasu kumburi a kafafuna, idan bana tafiya ba sa yi. Ko hakan da matsala?

Daga Halilu M.A Gaya

Amsa: Eh, ya kamata ka je likita ya ga wurin da ido kuru-kuru a tabbatar ba matsalar ba ce.

Me ke sa wa idan an ci nama sosai ake zawo?

Daga Shehu M.K. Kasuwar IBB

Amsa: Mu dai a likitance muna ganin matsalar daga kayan ciki ne. Wato kayan cikin dabba akwai kwayoyin cuta da dama a ciki, ta yadda idan ba a samu wanda ya iya aikinsu sosai ba, to fa ba za a wanke su sosai ba. Maimakon ma a wanke su sosai, muna ganin wadansu sukan bari kayan cikin su taba sauran nama wanda hakan zai iya gurbata naman. Ga shi kuma ka san naman Sallah ba wankewa ake ba, daga buhu ne sai tukunya, wato daga yanka sai kasko. To ka ga a nan ma da za a dan wanke shi da zai fi tsabta.

Sa’annan idan ma ya sauka, ba kowa ne ke iya jimirin wanke hannaye tsatsaf ba kafin a fara dandane. Dukkan wadannan muna ganin su suke jawowa a ci har da kwayoyin cuta, nan da nan cikin awanni a ji ciki ya kulle.

Shin da gaske ne tabar wiwi na kara lafiya? Idan tana kara lafiya me ya sa take haukata wadansu?

Daga Malam Kurma, Zariya

Amsa: A’a Malam Kurma ba dai kara lafiya ba. Ba a ce tabar wiwi na kara lafiya ba. Sai dai ko ka ce tana iya maganin wasu cututtukan. Domin a yanzu binciken kimiyya ya tabbatar akwai sinadarai a cikin tabar wiwi wadanda za su iya yin magungunan cutttuka da dama, musamman cututtukan daji. To ka ga ke nan da bambanci tsakanin karin lafiya da yin magani.

Kamar barasa ce ai an ce tana da illa kuma tana da alfanu, amma illarta ta fi yawa, don haka ake so a bar ta, to haka ma tabar wiwi, akwai alfanu akwai kuma illa, amma illar ta fi yawa.

Ina yawan jin jiri ko a zaune ko a tsaye ko idan na zo tashi. Kuma an yi mini awon jini da na zo ba da jini an ce daidai yake. Shin wata matsala na iya faruwa a jini a auna amma ba a ganta ba?

Daga El-Ishak M.

Amsa: Awon da suka yi maka ai kayyadaddu ne, ba dole su bayyana matsala ba. Wato awon yawan kwayoyin jinin da na ciwon hanta da na Sida watakila kawai ake yi idan ka zo ba da jini. Don haka ba a gama binciken jini ba. A wani hannu kuma, za a iya daukar jininka a yau a ce za ka iya bayarwa, amma idan ka bayar kai ma a wasu lokuta jinin naka zai iya yin kasa sai an kara maka ko a ba ka magungunan karin jini. Don haka dai tsugune ba ta kare ba.

Share