Da Dumi Dumi

Amsoshin tambayoyin daban-daban:   Kan tsabtar kwanuka da kofunan masu abincin sayarwa

Wadanne illoli ne za su iya samunmu idan muna sha ko cin abinci a kwanon da wadansu suka yi amfani da shi, kamar kofin mai shayi da kwanon mai tuwo

Daga Malam Yusuf Kaura

Amsa: Malam Yusuf har ka tuna mini da wani abu da ya faru da ni. Bari ka ji labarin. Ni ne dai na saba sayen shayi a wurin mai shayi a cikin flask, wato dan kurtun nan na ruwan zafi. Ran nan sai na je wani wuri bakunta na nemi kurtu a gidan na rasa, sai kawai na je na sha shayi haka kai-tsaye da kofin mai shayi. Ai in gaya maka washegari na tashi makogarona a daure yana ciwo. Da ma dai na kwana da shirin za a yi haka, don haka nan da nan na je aka duba ni aka ba ni magunguna. Na san za ka iya kara tambayar ko me hakan ke nufi. Abin da hakan ke nufi shi ne na kwashi kwayoyin cuta a kofin mai-shayin nan, wadanda suka tsaya mini a makogaro, har sai da na sha magani suka tafi. A wasu lokuta kwayoyin cutar a wadansu mutane sukan iya wucewa ciki su sa ciwon ciki da amai da gudawa. Sai daga baya ne na tuno cewa mai-shayin ba da soso da sabulu yake wanke kofunan da aka sha shayi da su ba, a ruwa kawai yake sa wa ya girgije.

Tun daga ranar idan ta kama, a cikin flask dina nake sayen shayi, ba na manta shi idan zan yi balaguro. To haka ma kwanon mai tuwo, da abina nake tafiya a sa mini a ciki in dawo gida in ci. To kai ma watakila haka ne ya fiye maka idan ka lura inda ake sayar maka da abinci ba kwanuka ko kofuna masu tsabta, kada su sa maka cututtuka.

Hakan fa amma bai hana ka ka saya ku ci da wani ko wadansu mutane da ka sani masu tsabta ne a faranti daya mai tsabta ba, in dai kowa ya wanke hannayensa sosai da ruwa da sabulu kafin a  zauna ci. Wannan zai sa a yi kira ga masu abincin sayarwa su tabbatar suna tsabtace kwanukansu da kofunansu kafin a zuba wa wani a ciki. A wanke sarai da ruwa da soso da sabulu a dauraye, a yarfe, idan ma ta kama a sa mayanin tissue a goge sarai kafin a ba wani kuma ya yi amfani da shi, domin gudun yada cututtuka.

ADVERTISEMENT

 

Tsakanin kifi da nama wanne ne jiki ya fi bukata?

Daga Sani Umar Malumfashi

Amsa: Dukkansu jiki yana bukatarsu daidai gwargwado, amma an fi son a fiye cin kifi fiye da nama, saboda kifi ya fi saukin kawo matsalolin kiba da maiko a jiki.

 

Idan dan Adam ya ci abinci kuma ya sha ruwa sukan zauna wuri daya ne a ciki?

Daga Abubakar Hassan, Kubau

Amsa: Eh, da ruwa da abinci mazauninsu daya. Na san watakila kana tambaya ce saboda an ce hanyar iska daban take da abinci da abin sha. To haka din ne, idan muka shaki iska takan shiga huhu ne, amma wani kaso yakan shiga ciki ya zauna, ya kasance a cikin ke nan dole akwai ruwa, akwai iska, akwai kuma abinci. Su ruwa da abincin ne kwata-kwata ba a so su shiga hanyar iska, don da sun doshi hanyar za a ji an kware ana tari.

 

Likita da gaske ne an fi jin yunwa da damina?

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja

Amsa: A’a a kimiyance babu wata hujja da kan yi nuni da haka

 

Shin da gaske ne idan mutum ya ji bayan-gida ya ki yi zai iya zama masa guba a ciki?

Daga Aliyu M.

Amsa: A’a ai ba a ciki bayan-gida ke zama ba, a babban hanji ne, inda da ma wurin ajiyarsa ke nan. Ba zai iya shiga wani wuri ba a jiki daga nan sai dai waje. Idan aka bar shi na tsawon kwanaki sai dai ya samar da abin da muke cewa taurin bayan-gida wato constipation.

 

Ni kuma idan na ci abinci sai in rika jin tashin zuciya. Ko me ke sa haka?

Daga Rabi I., Katsina

Amsa: Eh, wannan kam akwai dalili, wanda yawanci ciwo ne sai kin je an duba ki sosai.

 

Me ke kawo ciwon baya ga mutum, kuma ba bugewa ya yi ba, ba komai ba?

Daga Haruna U, Hadeja

Amsa: Ciwon baya ma akwai dalilinsa ko da ba a buge ba zai iya zuwa bagatatan. Yawanci kiba, tsufa, tsayi da rashin motsa jiki su suke kawo ciwon baya. Don haka yana da kyau a duba bayan naka a gani.

 

Ni ma ina yawan ciwon kafa, wani lokaci har ta kumbura ta yi dan dumi. Me ke kawo haka?

Daga Lubaba M.

Amsa: Shi ma wannan da alama ba lafiya ba, a rika jin ciwon kafa da kumburi har tana dumi, sai ka je an duba, akwai abubuwa da dama masu kawo haka, wadanda muka sha zayyanawa a wannan shafi.

 

Wane magani ne sahihi na ciwon kirji wanda zan samu a kyamis?

Daga Aliyu M. Katako, Jos

Amsa: A’a ai ciwon kirji babban suna ne, zai iya nuni da olsa, zai iya nuni da ciwon zuciya, zai iya nuni da wani ciwo a huhu. Don haka ba magani za ka tambaya ba, zuwa za ka yi a tantance maka me ke kawo maka wannan ciwo.

 

Me ya sa aka fi yawan fitsari da damina ko da sanyi?

Daga Muntaka L.

Amsa: Saboda idan gari ya yi sanyi, ba a bukatar ruwa a jiki sosai, sai koda ta yi ta fitsarar da shi.

 

Me ke kawo bugun zuciya?

Daga Mudassir Anchau

Amsa: Bugawar zuciya da sauri da sauri ko kuwa ciwon bugun zuciya? Domin suna da bambanci. Dukkansu dai matsaloli ne na zuciya. Bugawar zuciya da sauri-sauri alama ce ta wasu cututtukan jiki ko na zuciyar, wanda shi ne mutum zai rika yawan jin faduwar gaba. Amma ciwon bugun zuciya ciwo ne a karan kansa wanda alamunsa su ne mutum ya ji tsakiyar kirjinsa ya rike kamar an dora dutse, yana nauyi yana zafi, gumi na ketowa. Duk wanda ya taba jin daya daga cikin wadannan ko bugawar zuciyar da sauri-sauri ko alamun bugun zuciyar to ya tabbatar ya nemi inda za a binciki lafiyar zuciyar a gano ko mene ne.

 

 

 

 

Share