Da Dumi Dumi

Amsoshin tambayoyin daban-daban:  Tsakanin ruwan jikin mutum da jini wanne ya fi muhimmanci?

Tsakanin ruwan jikin mutum da jini wanne ya fi muhimmanci ta yadda idan ya kare mutum zai galabaita?

Daga Hannatu Nuhu

Amsa: A’a ruwa ai shi ne babban abokin tafiya wanda ya fi jini muhimmanci. Domin jinin ma ban da kwayoyin da ke cikinsa ai shi ma ruwa ne. Idan mutum ya zubar da jini sosai ana iya kara masa ruwa ya farfado ko da ba a kara jini ba.

Mene ne amfanin yin kaho da wadansu wanzamai ke yi su zuko jini?

Daga Jamilu M. Adam

ADVERTISEMENT

Amsa: Kaho ya samo asali ne tun shekaru dubbai da suka gabata a kasar Sin, inda suke amfani da shi wajen maganin matsalolin jini da ciwon jiki. Ka ga ke nan ba aikin likitancin zamani irin namu ba ne.

Na yi fama da tarin fuka. Na sha magani na wata shida ya tafi amma har yanzu ina fuka. Na koma asibiti likita ya ce ba a ba ni wani magani tunda na sha na tsawon watannin.

Daga A.Y. Argungu

Amsa: A’a akwai matsala mana wadda ya kamata likita ya kara dubawa. Musamman matsalar karancin jini. Ka san su magungunan sukan iya karar maka da jini. Watakila ko ba likita ba ne ya duba ka. Ka san a yanzu ba dole sai likita ne ke ba da maganin tarin fuka ba, sauran ma’aikatan lafiya ma za su iya bayarwa. Ka samu likita sosai ya kara aunaka ya rubuta maka gwaje-gwajen jini a gani ko daidai jinin yake.

Ni ma na yi tarin fuka na sha magani na warke. Shekaru biyu ke nan amma yanzu sai kafata take zafi take mini kamar wuta. Ina neman shawara.

Daga Ghali Mil 12, Legas

Amsa: Eh, kai ma kana bukatar ganin likita domin magungunan ciwon TB suna iya sa wannan matsala, ta hanyar karar maka da wasu bitamin na jiki. Sai ka je an duba an gani ko haka ne, a kuma ba ka wasu magungunan.

Me ya sa ne idona a kullum ja yake? Ba ya mini ciwo kuma ba ya kaikayi, kuma ina gani wasai. Ko akwai wata shawara da za a ba ni?

Daga Aminu Fari

Amsa: Watakila bambancin halitta ce kawai, akwai mutane da dama da na sani su idanunsu jajaye ne ba farare ba, kuma ba su da wata matsalar gani. Amma idan kana da shakku za ka iya zuwa likitan ido ya duba maka.

Shin mene ne sahihin maganin asma? Za a iya samunsa a kyamis?

Daga Aliyu Muhammad, Jos

Amsa: A likitance babu takamaiman maganin warkar da asma, sai dai mai sa ta lafa, wanda kuma ba a kyamis ake rubuta shi ba a asibiti ne. Sai an rubuta maka a asibiti sai ka zo kyamis ka saya.

Na lura akwai wasu cututtuka masu nasaba da yanayi ko? Don nakan ga a wasu lokuta wadansu mutane kan yi fama da cututtuka iri daya.

Daga Hassan Ibrahim Warji

Amsa: Eh, kwarai haka ne, yanayi na daya daga cikin abubuwan da kan kawo mana wasu cututtuka.

Idan na ci abinci sau uku a rana sai na rika gyatsa marar dadi da dare amma idan sau biyu na ci ba na yi. Sai kawai na daina karin kumallo. Shin hakan zai iya mini illa?

Daga Ummi Nagudu

Amsa: Eh, to in dai za ki dan sha ko da shayi ne ko koko ko kunu ai zai fi dacewa a ce ba ki sa komai a ciki ba. Wadannan kawai za su iya wadatarwa ba sai kin cika cikinki da wani abin karin kumallo ba.

Na ji wani likita yana magana a rediyo a kan hoton scanning da ake tura mutane, yana cewa akwai cututtukan da ba sai an yi musu ba kamar ciwon karshen hanji na appendid. Shin haka ne?

Daga Maman Sultan, Kaduna

Amsa: Eh, haka ne. A da ne sai an yi hoto, amma a yanzu koyarwar ita ce da marar lafiya ya nuna wurin da yatsa, likita ya taba wurin ya tabbatar shi ke nan kawai appendid ne.

Idan ina cin abinci makogwarona yana toshewa, sai da kadan-kadan yake tafiya, ko ruwa na sha shi ma da kyar yake wucewa. Me ke kawo haka?

Daga A’isha, Jigawa

Amsa: Eh, alamu ne na wata matsala. A likitance akwai cututtuka da dama da kan zo da matsalar hadiyar ruwa da abinci. Ki samu likita ya duba ki.

Jikina kan mini kaikayi ta yadda idan na sosai sai wurin ya tashi. Ko hakan wata matsala ce?

Daga Khadijah A. Kano

Amsa: Eh, alama ce ta borin jini. Magungunan rage kaikayi da za a iya samu a kyamis za su iya magance abin. Idan ba su yi aiki ba ne sai a ga likita.

Shin shan daci yana da illa ga lafiya? Domin ni idan ban sha ba ba na jin dadi

Daga Aminu T. Fagge

Amsa: Ya danganta da irin dacin da abin da ke cikinsa, domin akwai ’ya’yan itatuwa ko ganyayyaki da mukan ci masu daci amma ba su da illa, akwai kuma wasu masu daci da suke da guba. Don haka ya danganta da irin wanda mutane ke ci ne yau-da-kullum

Ni kuma wani abu na ga mutane suna shakawa a hanci. Ko mene ne amfaninsa?

Daga Malam Kurma, Zariya

Amsa: Kayan shaye-shaye ne kawai. Duk wani abu da ka ga ana sha ba ta hanyar da aka san ana cin abinci ko abin sha ba, kuma ba likita ne ya rubuta ba, shaye-shaye ne kawai. Ba za a ce kai-tsaye kayan maye ba ne tunda ba a san takamaimai mene ne ka gani ana shaka ba, amma dai akwai kayan maye da dama da ta hanci ake shakarsu.

Da na shaki angur sai na zo na bari, amma a yanzu ina ji hancina yana mini kamar dole sai na dawo da shaka. Shi ne nake neman shawara.

Daga Salisu Adamu, Bauchi

Amsa: To da alama ke nan kayan maye ka shaka, wato duk abin da za ka zo ka bari, jikinka ya dawo yana kewarsa, in dai ba abinci ba ne to kayan maye ne. Yadda za ka bari ka daina begensa sai ka nemi likitan kwakwalwa ya taimaka maka.

Share