✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ba za ta jira a aiwatar da karbar makaman Siriya ba

Wani gungun ’yan majalisar dattijan Amurka sun fara kulla alaka da hukumomin kasashe kan yadda za a kai wa Siriya harin soja, kafin Majalisar dinkin…

Amurkawa na adawa da kai wa Siriya hariWani gungun ’yan majalisar dattijan Amurka sun fara kulla alaka da hukumomin kasashe kan yadda za a kai wa Siriya harin soja, kafin Majalisar dinkin Duniya ta dauki matakin karbar makaman Siriya masu guba.
’Yan majalisar wadanda suka hada da abokan adawar Shugaba Barack Obama, sun fara baddala muhawarar da ake yi ta samun izinin kai hari don hukunta Shugaba Bashar al-Assad, kan zargin amfani da ya yi da makamai masu guba a kan al’ummarsa.
Wannan labarin ya fara kewayawa ne, bayan Obama ya gana da ’yan jam’iyarsa ta Democrat, a kokarin da yake yi na shawo kan ‘yan majalisar dattijai su amince, ya yi amfani da karfin soja a kan kasar Siriya.
Jami’an da ke taimaka wa ’yan majalisar, sun bayyana cewa sabon matakin da ake shirin dauka don kauce wa harin soja, shi ne, a yi hanzarin kwashe makaman Siriya masu guba, a danka su hannun Majalisar dinkin duniya, tamkar yadda kasar Rasha ta tsara. Sai dai Gwamnatin Amurka a fadar White House na ta nazarin kan al’amarin.
“A hakikanin gaskiya, shirin bayar da izinin amfani da karfin soja, zai kasance an gindaya sharadi, musamman idan shirin Rasha ya ci tura,” a cewar wani jami’i da ke taimaka wa wani dan majalisa, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
Matakan warware rikicin Siriya da Rasha ta gabatar wa Majalisar dinkin Duniya, na nufin Hukumar Tsaro ta Majalisar dinkin Duniya, ta gindaya sharadi, wadanda ta ce dole a cika su cikin lokacin da aka tsara, wato, a tabbatar da ganin makaman Siriya masu guba sun koma karkashin kulawar majalisar.
Shi ma wani mataimaki ga wani dan majalisar ya tabatar da cewa ana kokarin gindaya wa Assad da Mosko wa’adi, ta yadda za a tabbatar ba shigo-shigo ba zurfi suke yi wa Amurka da kawayenta ba.
Chuck Schumer, wani dan majalisar dattijai a karkashin tutar jam’iyyar Democrat, ya yi fatan wannan mataki da aka dauka zai “taimaka” wajen tabbatar da cewa “Siriya ta rabu da makamanta masu guba, ba tare da mun kai mata harin soja ba,” a cewarsa.
Jakadun kasashen Faransa da Birtaniya da Amurka sun tattauna kan wannan shirin warware rikicin da kasar Rasha ta gabatar, inda a kashin kanta ta bukaci Gwamnatin Assad ta mika makamanta.
Su kuwa ’yan tawayen Siriya, sun bayyana cewa idan har kasashen duniya ba su dauki amtaki ba, al’amura za su kara rincabewa. Domin Amurka ce kawai za ta iya hana Bashar Al-Assad amfani da makamai masu guba, a cewar Ahmad Al Jarba, Shugaban kungiyar ’yan juyin juya hali na Siriya, tare da shugaban ’yan tawaye Salim Idriss,  suka bayyana wa jaridar Washington Post.