✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka da Taliban sun kammala tattaunawa a Doha

An kammala zama na takwas a tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Kungiyar Taliban a Doha Babban Birin Katar. Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid a…

An kammala zama na takwas a tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Kungiyar Taliban a Doha Babban Birin Katar.

Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid a tattaunawarsa da tashar talabijin ta Aljazeera da ke Katar, ya ce a yammacin Talatar nan aka kawo karshen tattaunawar da ake yi a tsakaninsu da Amurka wadda ta dauki lokaci mai tsawo.

Mujahid ya ce tattaunawar na da tsayi kuma ta yi amfani kuma shugabannin bangarorin biyu za su yi shawara tare da daukar matakai a nan gaba.

A tattaunawa ta wayar tarho da Sarkin Katar, Tamim bin Hamd Al-Thani, ya yi da Shugaban Amurka, Donald Trump a ranar Talatar sun tabo batun ganawar Amurka da Taliban.

Cikin  watan Yuni, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce manzonta a tattaunawa da Kungiyar Taliban zai sake bude wata sabuwar tattaunawa da ’yan gwagwarmayar Taliban a kasar Katar, a wani kokarin rattaba hannu a kan yarjejeniyar da za ta kawo karshen yaki mafi tsawo da Amurka ta shiga.

A watannin da suka wuce, Mista Khalilzad ya gudanar da zaman tattaunawa da Taliban har sau bakwai, a kokarinsa na ganin an cimma yarjejeniyar da a karkashinta, Amurkar za ta janye dakarunta na farko da ta jibge a kasar Afghanistan, tun bayan hare-haren 11 ga Satumban 2001.

An yi imanin cewa, Amurka da Taliban sun amince da babban jigon bukatar mahukuntan birnin Washington tun daga shekarar 2001 da kuma a yanzu – wadda a ciki ake bukatar Taliban da kada ta sake masu tsaurin ra’ayi su sake samun damar mayar da Afghanistan mafakarsu.

A baya Kungiyar Taliban, wadda ta yi imani da izzarta ta fuskar karfin soji, ta yi watsi da bukatar tsagaita wuta a duk fadin kasar da Shugaba Ashraf Gani, ya yi mata tayi.

Cikin wani sakon da ba kasafai yake fitarwa ba, Shugaban Kungiyar Taliban Haibatullah Akhundzada, ya ce: “Bai kamata wani ya yi tsammanin mu ajiye makamanmu a fagen daga, ko kuma mu manta gwagwarmayarmu da kuma sadaukarwarmu na shekara 40, gabanin mu cimma muradunmu ba.”