✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka na keta hakkin dan Adam a Somaliya – Amnesty

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta ce hari ta sama da Amurka ta kai a Somaliya ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula…

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta ce hari ta sama da Amurka ta kai a Somaliya ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 14 wanda hakan ya saba wa dokar ’yancin dan Adam ta duniya.

Duk da cewa Amurka ta musanta zargin da ake yi mata amma a rahoton da Amnesty International ta fitar, ta bayyana cewa a hari biyar da Amurkar ta kai, an kashe fararen hula 14 da dama kuma sun samu raunuka.

A karkashin mulkin Shugaba Donald Trump, yakin da Amurka take yi da Kungiyar al-Shabab na kara kamari.

A bara, Amurka ta kai hari ta sama a Somaliya akalla sau 47.

Amma a bana abin ya wuce haka duk da cewa rundunar sojin Amurka da ke yaki a Nahiyar Afirka wato Africom ta bayyana cewa babu fararen hular da aka kashe.

Sai dai Kungiyar Amnesty ta ce tana da hujjojin da suka hada da hotuna da wadanda suka gani da ido da za su iyar shaidar hakan kamar yadda BBC ya ruwaito.

Rahoton na Amnesty ya ce akwai manoma uku ’yan kasar Somaliya da harin ya rutsa da su.

Kungiyar ta ce iyalan wadanda abin ya shafa ba su da wata hanya da za su bi wajen kai karar faruwar lamarin.

Duk da karuwar harin da ake kai wa al-Shabab, ita ke da iko da akasirin yankunan karkara da ke Kudanci da Tsakiyar kasar Somaliya