✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta kaddamar da rundunar yaki da ta’addanci a Afirka

An tsara yadda za a horas da sojojin na Afirka a fagen dabarun yaki.

A kokarin ganin an shawo kan matsalolin tsaro da suka hana zaman lafiya a wasu kasashen Yammacin Afirka, Amurka ta samar da rundunar da za ta yaki ta’addanci a nahiyar.

Amurka ta kaddamar da rundunar sojin ce da za ta taimaka wajen shawo kan barazanar tsaron da kasashen Yammacin Afirka da dama ke fuskanta daga mayaka masu ikirarin jihadi.

DW ya ruwaito cewa, rundunar dai za ta kunshi sojoji daga kasashe akalla ashirin da tara, inda ta soma gudanar da atisaye a kasar Ghana.

Bayanai sun ce an tsara yadda za a horas da sojojin na Afirka a fagen dabarun yaki a yayin atisayen rundunar da aka yi wa lakabi da Flintlock.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai hari tare da hallaka wasu sojoji Burkina Faso kimanin goma sha daya a yayin da suka yi yunkurin kwace iko da wasu garuruwa a yankunan Gabashi da Arewacin kasar a daren ranar Alhamis da ta gabata.

Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan masu gwagwarmaya da makamai.