Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Amurka ta karrama Ali Nuhu

Ali Nuhu
Ali Nuhu

Kasar Amurka karkashin ofishin jakadancinta da ke Abuja ta karrama fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan, Ali Nuhu Mohammed.

Kasar Amurka ta karrama jarumin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumunnta na Facebook a ranar Litinin da ta gabata.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce kasar ta karrama jarumin ne saboda nasarorin da ya samu wajen hidima wa Najeriya da kuma ’yan Najeriya.

Sanarwar ta ce Ali Nuhu wanda ake kira Sarkin Kannywood (Sarki Ali) fitaccen jarumi ne a masana’antar fina-finan Hausa, ya ba da umarni a dimbin fina-finai, ya kuma shirya fina-finai masu yawa a karkashin kamfaninsa mai suna FKD Productions.

ADVERTISEMENT

Kasar Amurka ta ce baya ga fina-finan da ya shirya da kuma ba da umarni, Ali ya kasance wanda ya shigar da matasa da yawa cikin masana’antar fina-finan Hausa, ya kuma kasance ubangidan jarumai masu yawa a masana’antar.

“Ya kuma yi fadi-tashi wajen kulla dangantaka a tsakanin Kannywood da Nollywood (Masana’antar Fina-Finan Turanci ta Najeriya). Kuma ya hada kai da daraktoci da furodusoshi wajen samar da fina-finan Hausa masu inaganci, inda a yanzu yake isar da sako a kan batutuwa masu muhimmanci ta hanyar ba da labarai a kansu,” inji sanarwar.

Kasar Amurka ta ce tana da masaniya kan irin lambobin yabon da Ali ya lashe a Najeriya da kuma duniya baki daya.