Da Dumi Dumi

Amurka ta samu bayanan sirri a daidai lokacin da Iran ke bunkasa makamashin Uranium

Yan Majalisun Amurka sun bayyana mabambantan ra’yoyin kan matakin barazanar da kasar Iran ke yi, bayan da tawagar jami’an tsaron kasa ta Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta gabatar da bayanan sirri ga ’yan majalisun baki daya.

“Sun bayyana mana yadda barazanar kasar Iran ke da bambanci da wadda aka gani a baya, kuma sun shaida mana cewa kai hari kan Amurka da abokan kawancenta na nan tafe,” a cewar Sanatan Jam’iyyar Republican Linsey Graham na jihar South Corolina, bayan wata ganawar sirri da ya yi da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da Mukaddashin Shugaban Ma’aikatar Tsaro Pat Shanahan da kuma Babban Hafsoshin Kasar Janar Joseph Dunford.

“Akwai alamun takala daga Iran da wadanda take ingizawa,” a cewar Shugaban Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Wakilai, Michael McCaul na jihar Tedas, inda ya ci gaba a cewa “tabbas muna da damuwa a kan sojojinmu wadanda ke fuskantar barazanar Iran, da kuma yiwuwar kai musu hari musamman ma a Iraki.”

Sai dai kuma ra’ayin ’yan Jam’iyyar Democrats ya bambanta kan wannan batun da kuma abin da ya sa Gwamnatin Trump ta kara matsa lamba kan Gwamnatin Iran da masu goya mata baya a Gabas ta Tsakiya.

A nata bangaren kuma, Iran ta ce ta ninka karfin makamashin uranium dinta sau hudu.

ADVERTISEMENT

Jami’an kasar Iran sun ce ana inganta makamashin uranium din ne domin makamashi da fararen hula ke amfani da shi, wanda bai kai karfin makamashin da aka amince wa da shi ba a cikin yarjejeniyar shekara ta 2015 kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Mai yiwuwa ba da dadewa ba Iran za ta zarce adadadin makamashin da aka bukaci ta adana a cikin wannan yarjejeniya.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya sanar a mako biyu da suka gabata cewa zai fice daga wasu bangarori na yarjejeniyar nukiliya tsakanin kasashe shidda, da ta hada da yanayin da Iran za ta iya sayar da wani adadin makamashin uranium ga wasu kasashe.

Rouhani ya yi barazanar Iran za ta iya kai wa matsayin kera makamai da makamashin idan ba ta samu sassaucin tattalin arziki da aka yi mata a yarjejeniyar ba kafin farkon watan Yulin bana.

Shi dai Shugaban Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar a bara. Ya kuma sake kakaba wa Tehran takunkumi sannan ya yi barazanar kara wasu a kan kasashe da suka ci gaba da kasuwanci da Iran.

Hakanan kuma idan ba a manta ba, Shugaban na Amurka ya yi wa Iran kashedi da kakkausar murya, yana mai barazanar fatattakarta idan ta kai wa Amurka ko kuma kawayen ta hari.

Trump ya fada a wani sakonsa na Tiwita cewa idan Iran tana so ta yi fada, toh karshenta ya kai a hukumance. Ya ce “ka da ki kara nuna wa Amurka yatsa.”

Ita ma kasar China ta sanya baki a lamarin, inda Shugaban Ofishin Harkokin Wajen Kasar Bang Yi ya yi Allah-wadai da Amurka game da takunkumin tattalin arziki da ta kakaba wa Iran.

Rahotanni da aka karbo daga ofishin Harkokin Wajen Kasar, sun nuna cewa Shugaban Ofishin Bang Yi ya gana da takwaransa na Iran Muhammed Cebad Zarif a Babban Birnin Bejin na China kamar yadda TRT ta ruwaito.

Mister Yi ya bayyana cewa kasashe biyun suna cikin hadin gwiwa, musamman a wannan lokaci da al’amura suke sauyawa cikin gaggawa.

Yi ya yi martani mai zafi game da takunkumin tattalin arzikin da Amurka ke wa Iran yayin da ya ce dole Iran ta kare kanta game da dukkan abubuwan da zai iya faruwa. Ya kara da cewa yarjejeniyar nukiliyar da aka yi tsakanin Amurka da Iran abu ne mai muhimmanci da ya kamata a kula da ka’idarsa sosai.

Shugaban Ofishin Harkokin Wajen Iran Zarif ya ce Tehran ba ta da laifi wajen warware yarjejeniyar amma a halin yanzu kasar China da Iran suna aiki tare domin ganin an dawo da yarjejeniyar.

 

 

 

Share