✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta yi gwajin makami mai linzami da aka haramta amfani da shi a duniya

Amurka ta yi gwajin wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango makonni  kadan bayan ficewarta daga wata yarjejeniyar makamin nukiliya da Rasha, wadda ta…

Amurka ta yi gwajin wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango makonni  kadan bayan ficewarta daga wata yarjejeniyar makamin nukiliya da Rasha, wadda ta haramta amfani da makamantansu.

Fadar Tsaro ta Pentagon ta ce ta gwada makamin ne kusa da gabar ruwan Kalifoniya a ranar Lahadi.

Rasha ta zargi Amurka da “kara rura wutar rashin jituwa.”

Amurka dai ta fice daga yarjejeniyar Intermediate-Range Nuclear Forces (INF) ranar 2 ga Agusta bayan ta zargi Rasha da saba yarjejeniyar, abin da Rashar ta sha musantawa.

Masana na ganin cewa karyewar yarjejeniyar ka iya haifar da gasar mallakar sababbin makamai a tsakanin kasashe.

Wannan yarjejeniya dai ta haramta amfani da makamai masu cin zangon kilomita 500 zuwa 5,500.

Pentagon ta ce makamin da ta gwada daga sansanin sojinta na ruwa na San Nicolas Island kusa da gabar ruwan Los Angeles, “na yau-da-kullum ne,” saboda haka bai kai girman nukiliya ba.

Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga Pentagon ta cew “Makamin ya bar doron kasa ne sannan ya bugi daidai inda aka harba shi bayan ya shafe sama da kilomita 500 a sama,” kamar yadda Ma’aikatar Tsaron Amurka ta bayyana.

“Bayanan da aka tattara daga gwajin za su bai wa Ma’aikatar Tsaro damar sake kera wasu makaman masu cin matsakaicin zang,” inji sanarwar.

Rasha ta kira gwajin da “abin nadama,” inda aka ambato Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Ryabkob yana cewa “Amurka tana yunkurin kara rura wuta ce kawai,” saboda haka “ba za mu mayar da martani ga takala ba. Ya kara da cewa ba za a shigar da Rasha cikin “tseren makamai ba.”

Kalamin nasa ya zo ne kwana guda bayan da Pentagon ta ba da tabaccin cewa Amurka ta yi gwajin.

A ranar Talata ce, Rasha ta soki Amurka game da gwajin makami mai linzamin wanda har zuwa makonni uku da suka gabata an haramta shi a karkashin yarjejeniyar makamai a tsakanin kasashen biyu.

Me ya faru da yarjejeniyar?

An zargi Rasha da saba ka’idojin yarjejeniyar a baya. Sai dai a farkon bana Amurka da Kungiyar NATO sun ce akwai hujjojin da ke nuna cewa Rasha ta fito da makaman 9M729 masu linzami.

Shugaban Kasar Rasha Bladimir Putin ya musanta zargin sa’annan ya ce kawai Amurka na kokarin amfani da haka ne domin ta fice daga yarjejeniyar.

A watan Fabrairu, Shugaba Donald Trump ya sanya 2 ga Agusta a matsayin wa’adin cewa kasarsa za ta fice idan Rasha ba ta bayar da hadin kai ba.

Makaman Rasha, samfurin 9M729 masu linzami suna firgita Amurka da kawayenta

Karyewar yarjejeniyar mai cike da tarihi ta jawo fargabar cewa hakan ka iya haddasa gasar kera makamai a tsakanin Amurka da Rasha da China.

An gano cewa wannan makami da aka harba ya zama wanda aka haramta amfani da shi a karkashin yarjejeniyar da aka yi da Rasha a 1987.

A wannan wata ne Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta  ce yarjejeniyar ta INF ta daina aiki.

Wacce ce yarjejeniyar?

Shugabannin tsohuwar Tarayyar Sobiyet, Mikhail Gorbacheb da na Amurka Ronald Reagan, a wancan lokaci su ne suka rattaba wa yarjejeniyar hannu a 1987

Yarjejeniyar da Amurka da Rasha suka sanya wa hannu ta haramta amfani da makamai masu cin gajere da matsakaicin zango, sai dai wadanda ake iya harbawa daga ruwa

Amurka ta damu da makaman SS-20 da Tarayyar Sobiyet take amfani da su a 1979, abin da ya sa Amurka ta jibge makamin Pershing a Nahiyar Turai – hakan ya jawo zanga-zanga

Zuwa 1991 kusan makamai 2,700 aka lalata

Kasashen biyu sun amince su rika bincikar aikace-aikacen junansu game da makaman.

Kuma zuwa 1991 an lalata makamai 2,700 a tsakanin kasashen.