Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Amurka za ta girke jirgin ruwan yaki a Tekun Pasha don gargadi ga Iran

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Gwamnatin Amurka, John Bolton, ya ce Amurka za ta girke katafaren jirgin ruwanta na yaki, mai suna, USS Abraham Lincoln Strike Group da  wata rundunar kai farmaki ta musamman, a yankin Tekun Pasha da zimmar aikewa da sako jan kunne ga mahukuntan Iran, cewa duk wani farmaki da Iran za ta kai wa kawayen Amurka a yankin za ta fuskanci fushin Amurka.

Hakan na zuwa ne, mako guda bayan Kamfanin Dillancin Labaran gwamnatin Iran ya wallafa wani hoto da wani jirgi mara matuki ya dauka da ta yi ikirarin cewa jiragen ruwa na yaki mallakar Amurka, suna matsawa kusa da yankin Tekun Pasha da ke Kudancin Iran.

ADVERTISEMENT

Mista Bolton ya ce yunkurin na zuwa ne don mayar da martani  kan take-take da takalar fada da ma neman rikici da Iran ke yawan nunawa a baya-bayan nan. Ko da yake, a cewar Mista Bolton, Amurka ba ta neman shiga yaki da gwamnatin Iran, amma a shirye take ta mayar da martani kan duk wani harin da dakarun juyin juya- hali na Iran ko  dakarun gwamnatin Iran za su kaddamar.

Sai dai kafar labarai ta ABC, ta ce, wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa kafar cewa girke mayakan da jiragen ruwa na yakin martani ne a kan take-taken da dakarun juyin juya-halin kasar da na gwamnatin Iran suke nunawa na yiyuwar kaddamar da farmaki.

ADVERTISEMENT

Amma a nata martanin, ta kafar talabijin gwamnatin Iran ta ce girke mayakan da kuma jirgin ruwan yakin da rundunar sojin ruwan Amurkar ta yi, ya yi kama da wani abu da take yawan aiwatarwa a kai-a-kai, kuma kalaman Mista Bolton kokari ne kawai na azizita al’amarin. Idan za a iya tunawa, a ranar 8 ga Afrilu, sashen hulda da jama’a na jirgin ruwan yakin ya bayyana cewa bangaren kaddamar da farmaki na rundunar ya bar sansanin sojin ruwan da ke Birginia a ranar 1 ga Afrilu a wani shirin girke jirgin da aka saba yi lokaci bayan lokaci. Don haka da’awar da Mista Bolton ya yi ta girke dakarun Amurka don mayar da martani a kan gargadin da Iran din ke yi, wani soki burutsu ne kawai, sakamakon mayakan  ruwa na Amurka sun dade da fara shirinsu a yankin, tun kafin Iran ta fara jan kunnen da take yi.

Iran dai ta kasance mai matukar suka a kan kasar Isra’ila da kuma yadda ke mara mata baya game da martanin da take mayarwa harin da ake kaiwa a yankin zirin Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran Iran (FARS), ya ruwaito Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Abbas Mousabi yana cewa gwamnatin Iran da kakkausar lafazi ta soki harin rashin nuna tausayi da gwamnatin Isra’ilar ke kaiwa a yankin Gaza. Sa’annan ya ce, sakamakon irin goyon bayan da Amurka ke bai wa mahukuntan Isra’ila da abin da ya kira abin ‘takaici’ yadda wasu kasashen Musulmi ke nuna halin ko-in-kula a kan yankin Falasdinu, babu yadda za a ce a wayi gari an taka wa Isra’ila birki game da miyagun laifuffukan da take yi a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.