✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta kori daliban da ke karatu ta intanet

Gwamnatin Amurka ta ce ba za ta kyale daliban kasashen waje su ci gaba da zama a kasar ba idan makarantun da suke karatu suka…

Gwamnatin Amurka ta ce ba za ta kyale daliban kasashen waje su ci gaba da zama a kasar ba idan makarantun da suke karatu suka fara bayar da cikakkun darussa ta intanet.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato wata sanarwa da Hukumar Shige da Fice da Hana Fasa-Kwauri (ICE) ta fitar tana cewa za a dauki mataki a kan daliban da abin ya shafa, ciki har da tasa keyarsu zuwa kasashensu na asali.

Sai dai hukumar ta bai wa daliban zabin komawa wasu makarantun don ci gaba da zama a kasar.

“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ba za ta bayar da biza ga daliban da za su yi karatu a makarantun da ke bayar da cikakkun darussa ta intanet ba; haka kuma hukumomin hana fasa kwauri da tsaron iyaka ba za su bar wadannan dalibai su shiga Amurka ba.

“Wajibi ne daliban da ke Amurka yanzu haka wadanda ke irin wannan karatu su fice daga kasar ko kuma su dauki wasu matakan, misali komawa makarantun da zaman aji ya zama dole idan suna son ci gaba da zama”, inji sanarwar.

Babu cikakken bayani a kan ko mutum nawa wannan lamari zai shafa, amma alkaluman hukuma na nuna cewa akwai daliban kasashen waje miliyan daya da dubu tara a Amurka a shekarar karatu ta 2018/2019.

‘Fakewa da guzuma ne’

Cibiyar Nazarin Ilimi ta Kasa-da-kasa da Sashen Kula da Ilimi da Bunkasa Al’adu na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ne suka bayyana hakan a wani rahoto da suka fitar a shekarar 2019.

Yayin da yake ambato wasu alkaluma na Ma’aikatar Ciniki ta Amurka, rahoton ya ce daliban kasashen waje sun bunkasa tattalin arzikin kasar da Dala biliyan 44 da miliyan 400 a 2018.

A cewar rahoton kuma, a shekarar 2018 akwai daliban Najeriya 13,423 a Amurka, wadanda suka ba da Dala miliyan 514 (Naira biliyan 184) don habaka tattalin arzikinta.

Sanarwar ta ICE na zuwa ne a ddaidai lokacin da wasu jami’o’i, ciki har da Harvard, suka bayyana shirinsu na mayar da darussa intanet saboda annobar COVID-19.

Masu suka sun ce wannan mataki ci gaba ne da yunkurin Shugaba Donald Trump na yin amfani da nonbar don hana shiga Amurka ta halaltacciyar hanya.