✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba jaririyar da aka haifa a jirgin kasa kyautar tikitin shiga jirgi na shekara 25

An bai wa jaririyar da aka haifa a cikin wani jirgi kasa na Ireland tikitin shiga jirgin kasa kyauta na tsawon shekara 25. Mahaifiyar jaririyar…

An bai wa jaririyar da aka haifa a cikin wani jirgi kasa na Ireland tikitin shiga jirgin kasa kyauta na tsawon shekara 25.

Mahaifiyar jaririyar ta haihu ne lokacin da jirgin yake hanyarsa daga birnin Galway zuwa garin Dublin da misalin karfe 3:05 na ranar Talatar da wuce.

An yi nasarar haihuwar jaririyar a cikin jirgin ne inda aka samu likita da ma’aikaciyar asibiti daga cikin fasinjoji wadanda suka taimaka wajen karbar haihuwar.

An kai mahaifiyar jaririyar da ’yarta asibiti bayan sun isa birnin Dublin na Jamhuriyyar Ireland kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.

Matukin jirgin Iarnród Éireann ya ce, an bai wa jaririyar da aka haifa tikitin shiga jirgi kyauta daga lokacin aka haife ta har zuwa tsawon shekara 25 sakamakon haihuwarta da aka yi a cikin jirgin lokacin da yake tafiya.

Daya daga cikin masu aikin yin abinci a cikin jirgin ta bayyana wa kafar  labarai ta Irish National Broadcaster (RTÉ) cewa, tana da masaniya game da mahaifiyar jaririyar kafin haihuwarta saboda ta ji lokacin da mai haihuwar ke nishi a ban-daki.

Ma’aikaciyar mai suna Emma Tote, ta ce ta bude kofar ban-dakin don ta ga wace ce a ciki sai ga budurwa, sai ta fada mata tana nakuda ne a wannan lokaci.

Misis Emma Tote, daga nan ta sanar wa direba cewa, ya kira motar daukar marasa lafiya, sannan suka tambayi sauran fasinjojin ko akwai ma’aikatan kiwon lafiya su matso kusa don taimakon wanda za ta haihu a cikin jirgin.

A cikin fasinjojin da suka ji sanarwa akwai wani likita mai suna Dokta Alan Debine da ke zaune a garin Galway.

Dokta Alan, ya ce ya fahimci cewa, wani abu na faruwa a lokacin da jirgin ya tsaya a tasharsa ta Kildare kusan minti goma sai aka sanar cewa, wata mata tana nakuda a cikin jirgin.

Dokta Alan, ya bayyana wa kafar labarai ta RTÉ cewa, mahaifiyar jaririyar ta fada hannun kwararrun ma’aikatan asibiti biyu, don haka suka ba ta agajin da take bukata.

“A lokacin da matar ke haihuwa na yi kokarin in je, in karbi haihuwar amma sai ta haihu minti 20 da yin nakuda,” inji Dokta Alan.

Dakta Alan, ya ce a lokacin da ake horar da shi a matsayin likita, yana iya karbar haihuwa. Amma wannan haihuwar ta zo ne, ba a muhallin da ya cancanci haihuwa ba, idan a asibiti ta haihu za ta samu kulawa ta musamman daga jami’an kiwon lafiya.

Kakakin jirgin Iarnród Éireann, ya ce: “Mun yi murna da godiya ga dukkan abokan huldarmu da suka taimaka mana wannan matar ta haihu lafiya a cikin jirgin.”