✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba Masar damar daukar nauyin gasar cin Kofin Afirka na 2019

A ranar Talatar da ta wuce ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta sanar da cewa an zabi Masar a matsayin sabuwar kasar…

A ranar Talatar da ta wuce ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta sanar da cewa an zabi Masar a matsayin sabuwar kasar da za ta dauki nauyin gasar cin Kofin Afirka ta bana (2019).

Gasar wacce za a yi a tsakanin ranakun 15 ga Yuni zuwa 13 ga Yuli, ana sa ran kasashe 32 ne za su fafata.

Shugaban Hukumar CAF, Ahmad Ahmad ne ya sanar da haka jim kadan bayan kwamitin shirya gasar ya kada kuri’a don zabo sabuwar kasar da za ta dauki nauyin gasar a tsakanin Masar da Afirka ta Kudu.

Masar ta samu yawan kuri’a 16, yayin da Afirka ta Kudu ta samu kuri’a daya kacal, yayin da mutum daya bai jefa tasa kuri’ar ba.

Tun farko an ba kasar Kamaru damar daukar nauyin gasar ce, amma ganin yadda ba ta shirya ba, ya sa Hukumar CAF ta kwace damar da ta ba ta a watan Nuwamban bara, inda ta bayyana cewa a ranar 9 ga watan Janairun nan ne za a sanar da sabuwar kasar da za ta dauki nauyin gasar.

Wannan shi ne karo na biyar da Masar za ta dauki nauyin  gasar.  Ita ce ta dauki nauyin gasar a 1959 da 1974 da 1986 da kuma a 2006 sai kuma a bana (2019).

A tsarin gasar, wannan shi ne karon farko da kasashe 32 za su fafata maimakon kasashe 16.

A halin yanzu Kamaru ce mai rike da kofin bayan ta lallasa Masar da ci 2-1 a gasar da aka yi a shekarar 2017.