✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An banka wa hedikwatar hukumar jiragen ruwa wuta

Fusatattun jama'a sun cinna wa Hedikwatar Hukumar Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) wuta

Fusatattun jama’a sun cinna wa Hedikwatar Hukumar Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) da ke Legas wuta da safiyar Laraba.

Kawo yanzu babu cikakken bayani, amma majiyarmu ta ce mutanen sun banka wa ofishin wuta ne a matsayin martani ga harbe-harben da sojoji suka yi kan masu zanga-zangar EndSARS a unguwar Lekki da dare.

Rahotanni sun ce jami’an kwana-kwanan NPA na kokarin kashe wutar ta aka sa wa ofishin.

Aminiya ta yi kokarin tuntubar kakakin hukumar, Jatto Adams, domin samun karin bayani amma bai amsa kiran waya ko sakon da aka aika masa ba.

Karin labarin na tafe.