✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bankado yadda China ke azabtar da Musulmin Uighur

Wasu bayanan sirri a China sun bankado yadda mahukuntan kasar ke tsananta matakan tsaro a sansanin yankin Dian jing a wani mataki na hana mutanen…

Wasu bayanan sirri a China sun bankado yadda mahukuntan kasar ke tsananta matakan tsaro a sansanin yankin Dian jing a wani mataki na hana mutanen da ke ciki wadanda galibi Musulmi ne ’yan kabilar Uighur tserewa duk da azabtarwar da suke fuskanta.

China na ikirarin cewa tana amfani da sansanonin na yankin Dian jing wajen koyar da karatu da sana’a ga al’ummar Uighur. An jima ana jita-jitar cewa tana amfani da damar ce wajen azabtar da Musulmi baya ga hana su ibada.

Bayanan sirrin wanda kungiyar ’yan jarida da ke binciken kwakwaf ta bankado, ya bayyana cewa gwamnatin China ta sanya tsauraran matakan tsaro ta yadda ake sanya idanu kan mu’amala da zirga-zirgar Musulmi  ’yan kabilar Uighur da ke tsare a sansanin.

Cikin matakan tsaron da China ke dauka a sansanonin rahoton ya nuna cewa hatta makewayi Musulmin na Uighur ba su da izinin zuwa face da rakiyar jami’an tsaro, matakin da ke nuna cewa ba su da damar ibada ko kuma ganawa da junansu.

Bankado asirin gwamnatin China na zuwa ne makwanni bayan jaridar New York Times ta wallafa wani labarin da ke cewa Shugaban China Di Jinping ya umarci jami’ansa da kada su nuna tausayi ga ’yan aware da masu tsautsauran ra’ayi, a wani jawabi da ya yi a shekarar 2014, bayan harin da ake zargin mayakan Uighur da kaiwa wata tashar jirgin kasa.

Kafin yanzu China tana musanta rahotanni daban-daban da ke nuna yadda take azabtar da Musulmi ’yan kabilar Uighur a sansanonin da take tsare da su a yankin na Dian jing, maimakon haka sai ta fake da cewa ta bude sansanin ne da nufin koyar da sana’o’i da kuma harshen Mandarin don rage tsattsauran ra’ayi ga Musulmin.