Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An bayyana manyan ayyukan da aka gabatar a Kagarko

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna Malam Ja’far Sani da Shugaban Qaramar Hukumar Kagarko yayin taron
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna Malam Ja’far Sani da Shugaban Qaramar Hukumar Kagarko yayin taron

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta kashe kimanin Naira biliyan 5.73 wajen bayar da kwangiloli da gudanar da ayyuka a fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma gyare-gyaren hanyoyi da sauransu.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna Malam Ja’afar Ibrahim Sani ne ya bayyana haka a dakin taro na Karamar Hukumar Kagarko, inda ya gana da masu ruwa-da-tsaki don bayyana musu irin ayyukan da gwamnatin ta gudanar cikin shekara uku.

ADVERTISEMENT

Kwamishinan ya ce Naira biliyan daya da miliyan 100 aka kashe a bangaren ilimi wajen gina makarantar sakandaren kimiyya guda daya da samar da ajujuwa 23 da wutar lantarki mai amfani da hasken rana guda 13 da gina makewayi 11.

A fannin kiwon lafiya kuma Kwamishinan ya bayyana cewa an kashe kimanin Naira miliyan 267 da dubu 100 wajen gyara babban asibiti da kuma kananan asibitoci 10 da ke sassan karamar hukumar. Bangaren manyan ayyuka kuma, ya ci Naira biliyan 4 da miliyan 300, inda aka kashe su wajen yin hanyoyi shida da kuma kare zaizayar kasa.

ADVERTISEMENT

Ya jinjina wa mutanen karamar hukumar tare da yin kira gare su da su ci gaba da kare kambinsu na kasancewa karamar hukuma mafi zaman lafiya a Kudancin Kaduna.

Yayinda yake jawabi, tun da farko, Shugaban Karamar Hukumar, Mista Nasara Rabo, jinjina wa gwamnatin jihar ya yi kan namijin kokarin da take yi wajen sauke nauyin da ke wuyanta don inganta rayuwar talakawanta.

Da aka bai wa mahalarta damar yin tsokaci da  tambayoyi, Hassan Machu, wani manomin citta da ya yi magana a madadin masu noman citta na karamar hukumar, ya yi kira ga gwamnati ta tallafa wa manoman citta da iri da magungunan feshi da kuma taki don kara bunkasa harkar noman da ya ce ba su kadai manoma ba, hatta gwamnati za ta samu karin kudin shiga ta hanyar noman.

Shi kuwa da yake mika nasa korafin, wani nakasasshe da ya yi magana a madadin nakasassun karamar hukumar, Andrew Makeri, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta debi ma’aikata a cikin nakasassun da suke da horo kan koyar da sana’o’i don koya wa daliban makarantun firamare yadda za su rika sana’anta abubuwan da za su rika kaiwa makaranta a matsayin sana’ar hannu, ba wai su buge da sayen kwalin alli da sabulu da takardu suna kaiwa a matsayin sana’ar hannu ba.

Kungiyoyin addinai da na mata da matasa da na ’yan kasuwa da nakasassu da sarakuna da kuma shugabannin al’umma ne suka halarci taro.