Da Dumi Dumi

An binne Robert Mugabe a kauyen Kutama

An binne tsohon Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a mahaifarsa da ke Kutama, makonni uku bayan mutuwarsa.

Tsohon Shugaban wanda ya mutu yana da shekaru 95, an binne shi ne a harabar gidansu na gado da ke kauyen Kutama a kasar, mai nisan kilomita 90 daga Harare babban birnin kasar Zimbabwe.

Mugabe, dai ya mutu a wani asibiti da ke kasar Singapore a ranar 6 ga watan Satumba bayan ya yi fama da jinya, kusan shekaru biyu kenan bayan hambarar da gwamnatinsa da ya shafe shekaru 37 yana jagoranta.

An dade ana tafaka muhawara tsakanin gwamnatin kasar da kuma iyalan Mugabe kan takamaiman wurin da za a binne mamacin. Daga karshe gwamnatin kasar ta bayar da kai bori ya hau inda ta amince da ra’ayin iyalan Mugabe na binne shi a mahaifarsa da ke Kutama.

Rahoton BBC.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya