✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An birne mutum 18 da ’yan bindiga suka kashe yau a Katsina

An birne gawarwakin mutum 18 da ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla yau Laraba a kauyen `Yar Gamji a karamar hukumar Batsari jihar Katsina.…

An birne gawarwakin mutum 18 da ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla yau Laraba a kauyen `Yar Gamji a karamar hukumar Batsari jihar Katsina.

An birne gawarwakin ne a makabartar Dan Takum bayan yi masu sallar jana’iza a fadar Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, Hakimai da wasu masu rike da sarautu tare da jami’an gwamnati da kuma sauran jama’ar gari suka halarcin sallar jana’izar.

Limamin babban masallacin Katsina, Ustaz Mustapha Ahmed, ne ya jagorancin sallar jana’izar.