Da Dumi Dumi

An buɗe gidan zoo na farko mai zaman kansa a Katsina 

A kwanakin baya ne aka buɗe gidan adana namun daji da aka fi sani da gidan Zu da wajen shaƙatawa tare da ma’aikatar sarrafa tumatiri na farko masu zaman kansu, wanda matashin ɗan kasuwa, Dokta Muhammad Usman ya kafa ƙarƙashin kamfaninsa na Aldusar.

Bikin buɗe wannan kamfani da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya yi, ya zamo irinsa na farko a Jihar Katsina wanda ba mallakin gwamnati ba. Kamar yadda Gwamna Masari ya ce, da ma ‘yan kasuwa ke ɗaukar aiki ba gwamnati ba. “Ita gwamnati dama take bayarwa ga ‘yan kasuwa domin su yi kasuwancinsu cikin lumana tare da dokokin da za su taimaka wa kasuwancinsu ya bunƙasa. Ta wannan hanyar ce zai sa al’umma su samu aikin yi. Ya kamata mutane su fahimta cewa, in an ce mutum ya samu aikin yi ba wai ana nufin ofishin gwamnati ba, a’a, ya samu wani abu wanda zai riƙe don ya tsare mutuncinsa ta hanyar ciyar da iyalansa tare da yi masu hidimomi a cikin kwanciyar hankali. Wannan shi ake nufi da mutun ya samu aikin yi.”

Gwamnan wanda ya jinjinawa Dokta Muhammadu a kan wannan namijin ƙoƙari, har ila yau ya kawo misali da shirin bayar da rance da wannan kamfanin sarrafa tumatir ya ɓullo da shi a tsakaninsa da manoman tumatiri na jihar ta hannun shugaban kungiyar masu noman tumatirin, wanda ake sa ran sama da mutane 5000 za su samu aikin yi idan aka lura da yadda noma yake.“Hanyar da za a farfaɗo da tattalin arziƙin jama’a babu kamar noma da kiwo wanda ke ɗaukar a ƙalla kashi 70 cikin ɗari na jama’ar Jihar Katsina.”

Da ya juya ga batun gidan adana dabbobin, Gwamna Masari ya ce “shi ne abu na biyu mafi amfani domin mafi yawan yaran da ke karatu, wasu ma daga cikinsu har sun kai ga shiga jami’a in an ɗebe irinsu rakumi, sa, jaki ko doki ba su san wasu dabbobin ba sai dai ko a littafi ko kuma a sinima amma yau ga su har cikin gida an kawo inda za a gan su a fili, wasu ma sai dai a ji labarinsu. Wannan gidan Zu zai sa yaranmu su samu damar ƙara ilmi na hakika a kan batun dabbobi.

“A nan ina so in yi kira ga iyayen yara da su riƙa kawo su wannan waje domin shaƙatawa tare kuma da buɗe ido kuma da ƙara buɗe musu ƙwaƙwalwa wajen neman sanin abubuwa.

ADVERTISEMENT

Shi kuwa matashin ɗan kasuwar, Dokta Muhammadu Usman Sarki cewa ya yi,” kamfanin Aldusar zai sama wa al’umma sama da dubu ɗaya aikin yi. Har ila yau manoma sama da dubu biyar za su samu aiki domin an assasasa wannan kamfani na tumatiri ta yadda zai sarrafa tan dubu 3 a kowacce sa’a, a rana zai sarrafa tan dubu 72 kwatankwacin mota tirela ukku.

“Kazalika, mun ɓullo da shirin bayar da rance a wannan kamfani tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Manoma tumatiri ta jiha, inda manoma ɗari 3 suka amfana da wannan shiri inda muka ba su kayan noma da nagartaccen iri domin haɓaka noma a jiha da kasa baki ɗaya.”

Da ya juya a batun gidan Zu, ya ce wannan shi ne waje na farko a cikin Jihar Katsina ko ma a Arewa maso yamma da za a ce ƙarƙashin wani kamfani ba gwamnati ba da aka gina.

Shugaban kamfanin ya ci gaba da cewa ya yanke wannan shawara ce ta bude gidan Zu da wajen shaƙatawar yara har ma da manya domin ba al’ummar Jihar Katsina damar ziyartar gani da ido musamman a kan abin da ya shafi ajiye namun daji na gida da na waje. Kuma wannan na nuni da yunƙurinsa na ganin cewa ba a bari wasu dabbobin ko tsuntsaye suna ɓacewa ba, musamman a irin waɗannan yankuna. Ya gode wa Gwamna Masari akan irin gudunmuwar da ya riƙa ba shi ta shawarwari da haɗin kai gami da ziyatar wajen da shi ya riƙa yi a lokacin da ake cikin aikin gina kamfanin har zuwa wannan rana da aka buɗe shi.

Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar shi ne shugaban taron buɗe wannan kamfani na Aldusar. Ya ce waɗannan ayyuka biyu da shi wannan kamfani ya kawo suna da muhimmaci ga ci gaban Jihar Katsina tare da tattalin arzikinta. “Hakika Jihar Katsina jihar noma da kiwo ce kuma mun ji irin faɗi tashin da gwamnati ke yi na farfaɗo da harkar noma, wanda noman tumatir na daga cikin abin da ke jawo wa manoma zurarewar kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje, domin idan ka ji labarin bilyoyin nairorin da ake kashewa don shigo da tumatirin, abin zai sa ka cikin firgici bayan kuma ga shi a nan. Idan kakar tumatiri ta zo a nan Jihar Katsina kaɗai tumatirin da yake ruɓewa ko a yi kauɗa da shi koma a zubar ana yin asarar bilyoyin kuɗi. To sai ga shi Allah Ya ba Dokta Muhammadu fikirar da ya kafa wannan kamfani na sarrafa tumatir, lallai wannan abin a yaba masa ne ƙwarai da gaske. Kazalika, buɗe gidan Zu ba ƙaramin aiki ba ne in muka yi la’akari da ciyar da dabbobin da kula da lafiyarsu.”

A ƙarshe Babban Jojin kuma shugaban taron ya yi fatan samun tallafi daga gwamnati ta yadda za ta ƙara ba shi wannan matashin ɗan kasuwa damar ƙara buɗe wasu wuraren da zasu kawowa Jihar da Ƙasa cigaba,domin a cewarsa,akwai kayan amfanin gona iri-iri a Jihar ta Katsina da za’a iya sarrafawa kuma a fitar da su ƙasashen waje.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya