✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude filin wasa a garin Dawakin Kudu

A ranar Litnin da ta gabata ce  Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya bude wani karamin filin wasa da ke garin  Dawakin Kudu a…

A ranar Litnin da ta gabata ce  Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya bude wani karamin filin wasa da ke garin  Dawakin Kudu a Jihar Kano.

Filin wasan wanda Gwamnatin Tarayya ce ta gina shi an fara gininsa a shekarar 2017 da nufin samar da kayyakin wasanni ga jihohi don bunkasa harkar wasanni a kasa baki daya.

Minista Dalung ya bayyana gamsuwarsa game da yadda aka gudanaar da aikin filin wasan inda kuma ya damka ragamar gudanar da filin wasan ga Gwamnatin Jihar Kano.

Har ila yau Ministan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano ta ci gaba da kula da filin don ganin ya taimaka wajen samar da hazikan ’yan wasa a nan gaba.

Bayan kammala bude iflin wasan ne aka kuma rarraba kayayyakin wasanni na kimanin Naira dubu 120 ga kowace hukumar wasanni da ke kananan hukumomin jihar 44.

Dimbin ’yan wasa da masoya wasanni ne suka halarci bikin bude sabon filin wasan.

Haka kuma an gudanar da kwarya-kwaryar wasan kwallon kafa a  sabon filin a tskaanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Gladano FC inda Kano Pilars ta yi nasara da ci daya mai ban haushi a bugun da ga kai sai mai tsaron gida.

A karshen bikin ne aka ba kungiyar kwallon kafa na Kano Pillas kofi don girmamawa.