✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude jigilar jiragen sama zuwa kasashen waje

Najeriya za ta ci gaba da sufurin jiragen sama na kasa da kasa daga ranar 29 ga Agusta

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta bude jigilar jiragen sama na kasa da kasa daga ranar 29 ga Agusta, 2020.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika ya sanar da haka da yammacin Litinin 17 ga Agusta 2020 ta shafinsa na Twitter, mako biyu kafin bude filayen jirgin.

“Za mu fara da Legas da Abuja kamar yadda muka yi a lokacin bude sufurin jirage na cikin gida. Nan gaban za a sanar da tsare-tsaren da kuma matakan da aka tanada. Muna godiya bisa hakurin da  kuka nuna”, inji shi.

Wakilinmu ya ruwaita ministan na sanar da haka a lokacin taron jawabin kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19.

Ya ce idan aka bude filayen bayyan mako biyun masu zuwan, za a ci gaba da bin sauran matakan kariya da suka hada da bayar da tazara da dangoginsu.

Tun a watan Fabrairu Gwamnatin Tarayya ta rufe dukkannin tafiye-tafiyen jiragen sama da na kasa domin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Cutar ta fara bulla a Najeriya ne a jikin wani bako dan kasar Italiya da ya shigo kasar da ita ta filin jirgi na Legas.

Ba a gane yana dauke da cutar ba sai bayan sa’o’i kuma daga nan aka yi ta samun karuwar masu ita a kasar.