✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude kasuwanni, za a koma aikin gwamnati a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umarnin bude kasuwannin mako 15 wadanda ta rufe a yunkurinta na kare yaduwar annobar coronavirus a jihar. Ta kuma…

Gwamnatin jihar Katsina ta ba da umarnin bude kasuwannin mako 15 wadanda ta rufe a yunkurinta na kare yaduwar annobar coronavirus a jihar.

Ta kuma umarci daukacin ma’aikata da su koma bakin aiki daga ranar Litinin 8 ga wata.

Kasuwanin da aka ba da za a bude su ne wadanda akasarinsu ake hada-hadar kayan abinci da dabbobi daga ciki da wajen kasar nan.

Kasuwannin sun hadar da kasuwar Maiadua, Mashi, Dandume, Zango, Danja, Bakori, Yankara, Kafur, Dankama, Kaita, Kagadama, Dutsi, Garkin-Daura da kasuwar Kayawa.

A sanarwar da Sakataren Gwamnatin jihar Mustapha Inuwa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce umarnin bude kasuwannin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a, 5 ga watan Yuni 2020.
Mustapha Inuwa ya ce matakin ba ya nufin babu cutar coronavirus a jihar, don haka ya yi kira ga al’umar jihar da su kula da matakan kariyar annobar.

Ma’aikatun gwamnati za su koma aiki

Gwamnatin jihar ta kuma umarci daukacin ma’aikanta da na kananan hukumomi da su koma bakin aiki daga ranar Litinin, 8 ga watan Yuli.

Wannan umarnin na cikin sanarwar da Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Ma’akatan Gwamnatin jihar, Ado Dutsinma ya fitar.

Umarnin a cewar sanarwar ya biyo bayan sassaucin da aka yi wa daukacin dokar kulle a jihar Katsina ne.

Sanarwar ta bukaci daukacin sakatarori da shugabannin ma’akatun jihar da su tabbatar ma’aikata na bin ka’idojin komawa bakin aiki kamar yadda aka tsara.

Ka’idojin da suka hadar da matakan kariyar cutar coronavirus, sannan dole ma’aikata su rika sanya takunkumin rufe baki da hanci tare da ba da tazara a lokacin da suke bakin aiki.