Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An bukaci al’umma su yawaita addu’a

Alhaji Usman Ibrahim

An roki al’ummar kasar nan da su kara zage damtse, wajen yin addu’a ga ci gaban kasar nan da kuma wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Babban jami’i a kungiyar tabbatar da nasarar Muhammadu Buhari da Osinbajo (MBODSG), Alhaji Usman Ibrahim shi ne ya yi wannan kira, inda ya ce sanin kowa ne an samu kyakkyawan ci gaba a fannoni da dama a kasar nan a zangon farko na mulkin Muhammadu Buhari, mussaman a kan cin hanci da rashawa, dakile ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram, samar da hukumar raya shiyyar Arewa maso gabas da batutuwa da dama.

ADVERTISEMENT

Ya ce wannan gwamnati a zango na biyu ta yi tanadi masu alfanu ga al’ummar kasar nan, wadda da zarar ranar 29 ga wata an rantsar da ita.

Ya ce matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a wasu jihohin kasar nan, “na yin garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan ta’adda a jihohin Zamfara da Katsina duk, cikin ikon Allah sun zo karshe, amma akwai bukatar sai mu dage da yawaita addu’o’i, mussaman cikin wannan wata na Ramadan.” Ya ce babu wani abu da ya gagari Ubangiji.

ADVERTISEMENT

Ya kuma yi kira ga ‘yan adawa da su rika yin adawa mai ma’ana, ba kame-kame ba kuma su jira hukuncin da kotu za ta yanke, tun da lamarin karar ta su da suka shigar tana gaban kotu amma yin wasu kalamai ko zargin shugabar kotun, duk ba shi da wani amfani, ko kuma yin wasu kalamai da ba su da ma’ana. Ya ce kowa ya san wannan gwamnati ta kudiri aniyar ci gaba da aiwatar da tsare -tsaren da za su inganta rayuwar al’ummar kasar nan da kuma tabbatar da dauwamamen zaman lafiya.

Daga nan sai ya ce yana da yakinin sanin cewa Buhari dattijo ne, wanda yake da al’ummar kasar nan a zuciyarsa kuma a shirye yake don ganin jama’a sun sami sauki ta kowane bangare, domin babu abin da Shugaban Kasa yake bukata illa addu’ar daga al’umma wannan kasa.