✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci mata su kaurace wa yin kunshi kafin lokacin zabe

An jawo hankalin mata  kan su kauce wa yin kunshi gab da lokacin zabe, domin zai hana na’urar zabe ta tantance su, balle su samu…

An jawo hankalin mata  kan su kauce wa yin kunshi gab da lokacin zabe, domin zai hana na’urar zabe ta tantance su, balle su samu damar zaben ’yan takarar da suke so.

Jigo a Jam’iyyar APC daga mazabar Wakilin Kudu 1, a Karamar Hukumar Katsina ta Jihar Katsina, Malam Bishir Yakubu ne ya yi wannan kira, jim kadan da kammala rangadin yakin neman zabe da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya gudanar a dukan kananan hukumomi 34 na jihar.

Malam Bishir Yakubu wanda kuma shi ne Kauran Bwari ya nuna farin ciki da godiya ga dubban magoya bayan Jam’iyyar APC da suke nuna kauna da soyayyarsu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Katsina da kuma dukan ’yan takarar mukaman siyasa na jam’iyyar.

Ya yi kira ga dubban magoya bayan Jam’iyyar APC a Jihar Katsina su fito kwansu da kwarkwatarsu su yi wa ’yan takarar kujerun siyasa na jam’iyyar ruwan kuri’a a zabubbukan da ke tafe domin samun nasara.

Ya yi kiran a ci gaba da nuna hadin kai da kauna da kuma soyayya ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Katsina domin kara more mulkin dimokuradiyya da kuma samun turba mai ma’ana domin amfanin al’umma baki daya. Ya  jawo hankalin al’umma da magoya bayan APC cewa su yi la’akari da  nasarori da ci gaban da jam’iyyar ta kawo a matakin tarayya da  jihar a shekara uku da rabi da suka gabata, irin su inganta wutar lantarki da kyautata tattalin arziki da gyarawa da kuma giggina hanyoyin motoci da samar da hanyoyin jiragen kasa da giggina cibiyoyin kiwon lafiya da makarantun zamani da kuma jan damara ta fuskar ciyar da bangaren tsaro gaba da makamantansu.

Ya nuna jin dadinsa kan yadda magoya bayan  suka bayar da gagarumar gudummawar da  taimakawa wurin yakin neman zaben ya gudana cikin nasara da kwanciyar hankali a daukacin kananan hukumomi 34 na Jihar Katsina, ba tare da tayar da hankalin kowa ba balle fadace-fadace ko doke-doke.

Alhaji Bashir Yakubu ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari saboda kyakkyawan shugabancin da suke gudanarwa domin ci gaban al’umma.