✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci Ministan Ilimi ya waiwayi Kwalejin Ilimi ta Zariya

An bukaci Ministan Ilimi da ya ceto Kwalijin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya daga halin tabarbarewa na rashin iya gudanarwar shugabanci. Masu ruwa da…

An bukaci Ministan Ilimi da ya ceto Kwalijin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya daga halin tabarbarewa na rashin iya gudanarwar shugabanci.

Masu ruwa da tsaki a harkar ilimi ne suka yi kiran tare da ma’aikata da kuma al’umomin da ke makwabtaka da kwalejin wato FCE, Zaria.

Masu korafin sun ce akwai matsalar rashin kayan koyarwa da rashin ruwa ga dalibai musamman masu kwana a makaranta da kuma rashin wutar lantarki.

A wani bincike da suka gudanar ya nuna cewa babu wata Kwalejin Ilimi ta Tarayya a Arewacin Najeriya da dalibai ke biyan kudin makaranta kamar Kwalejin Ilimin ta Zariya.

A bangaren ma’aikata da malamai, suma sun koka ne kan kudaden alawus daban-daban har na wata 22 da suke bin mahukuntan makarantar bashi.

Aminiya ta gano  cewa sakamakon umurnin da Gwamnatin Tarayya na biyan albashi na bai daya, daukacin masu gadin kwalejin yanzu sun zama cikakkun ma’aikata saboda a rufe rarar kudin da ake karba a duk wata da sunan biyan albashi wanda a baya ma’aikatan wucin gadi ne.

A dalilin hakan ma wasu da aka ba su takardar daukar aikin kusan shekara guda da ta wuce suna aikin ne kuma ba a biyansu albashi, amma daga 28 ga watan 11 na bana ranar da masu tantancewan na IPPIS suka fara sai gashi yanzu an saka su a tsarin ma’aikata na IPPIS.

Aminiya ta tattauna da dama daga cikin dalibai da malamai da ma’aikata da kuma makwabtan makarantar akan halin da suke ciki, inda da dama daga cikinsu suka nuna rashin jin dadinsu na yadda mahukunta makarantar suka yi watsi da duk wani al’amari da ya shafi halin da dalibai da malamai da kuma makwabtan makarantar suke ciki.

Aminiya ta ji  cewa ko a kwanakin baya al’ummar Gyallesu sun toshe kofar shiga kwalejin da shara domin su jawo hankalin masu ruwa da tsaki a makarantar don su saurari kokensu.

Wakilin Aminiya ya ji ta bakin Shugaban Kwalejin Dokta Ango Abdullahi Ladan akan korafe-korafen da al’umma ke yi akansa, inda ya ce,”Maganar alawus din ma’aikatan an biya su kusan kashi 80 daga cikin dari na duk wani bashi da suke bi, sannan maganar wutar lantarki shi ma an ingantashi fiye da yadda yadde yake a da, haka ruwan sha shi ma mun yi musu babban rijiyar burtsatse wanda har mun fitar wa da mutanen Gyallesu da kan fanfo wanda suke amfana da shi.”

Ya kara da cewa, “Lallai su al’ummar Gyallesu sun nemi da mu zauna amma ka san soboda irin zirga-zirgan da aiki ke sawa, don haka ban samu damar zama da su ba sai dai mataimakina ya zauna da su kuma duk abin da suka tattauna da shi tuni mun fara daukar matakin gyara.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Shugaban Kungiyar Malamai ((COEASU) na makarantar, Haliru Musa, amma abin ya ci tura