✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci Musulmi su nemi ilimi a bikin baje kolin littattafan Musulunci

Malamin addini kuma Daraktan Kamfanin Samar da Tsaro na Mado Security, Alhaji Abdurrazak Animashun ya bukaci Musulmi su nemi ilimi don sanin yadda za su…

Wadansu a wurin baje kolin littattafan musulunci da kamfanin De Minaret ya shirya a Abuja a ranar Asabar da ta gabata  Malamin addini kuma Daraktan Kamfanin Samar da Tsaro na Mado Security, Alhaji Abdurrazak Animashun ya bukaci Musulmi su nemi ilimi don sanin yadda za su gudanar da addini ba tare da sun jahilce shi ba.      
 Ya bukaci hakan ne yayin bikin baje kolin littattafan musulunci da Kamfanin De Minaret International ya yi a Abuja Asabar da ta gabata.
Ya ce: “A yanzu jama’a musamman ma Musulmi ba sa son karance-karance, kuma babu wani yunkuri daga kowane bangare don ganin an shawo kan wannan al’amari. An yi sakaci sosai, domin jama’a sun fi mayar da hankali kan shiga intanet, inda suke bata lokaci a facebook da twitter da sauransu, hakan abin bakin ciki ne.
“Yadda za mu yi amfani da ilimi ya danganta da hikima, hikima kuma kan kasance mai amfani idan an hada da ilimi, don haka ya zama wajibi mu nemi ilimi. Kuma wannan baje kolin ba wai don sayar da littattafai ba ne kawai, a’a, don a samar da ilimi a kuma gina al’umma ne, kasancewar babu inda mutum zai je matukar ba shi da ilimi. Don haka ya zama wajibi matasa su nemi ilimin addini da kuma na boko don su samu tsira, kasancewar Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda yake neman duniya, ya nemi ilimi; wanda yake neman lahira ya nemi ilimi, haka kuma duk mai neman duniya da lahira to shi ma ya nemi ilimi.
Shugaban Kamfanin De Miniret, Dokta Saheed AbdurRa’uf (Abu Mazeedatil Khayr) ya ce sun shirya baje kolin litttattafan Musulunci don su cusa wa Musulmi dabi’ar karance-karance.
 Ya ce: “Mun shirya wannan baje koli na kwana goma ne don mu cusa wa Musulmi dabi’ar karance-karance. A wannan baje kolin mun samar da littattafai fiye da dubu 15, wadanda muka shigo da su daga kasashe da suka hada da Saudiyya da Lebanon da Birtaniya da Masar da Siriya da Iran da sauransu, kuma mun rage kashi 15 zuwa 30 na farashinsu.”
Hajiya A’isha Bello Mustapha mai karanta labarai a gidan talabijin na NTA, da ta halarci bikin bude baje kolin ta ce, Musulmi za su amfana da wannan baje kolin, tun da akwai littattafan Musulunci da suka kunshi komai da komai na rayuwa, kuma Manzon Allah (SAW) ya ce mu nemi ilimi ko da kuwa a birnin Sin ne.
A bangaren littattafan yara akwai littafin ‘kur’an stories for Little Hearts’ da ‘kur’an and Seerah Stories for Kid’ da ‘Islamic billage Stories’ da ‘Welcome Ramadan’ da sauransu.
Littattafan zamantakewa kuma akwai ‘The Muslim Parent Guide’ da ‘A Guide for Young Muslim’  da ‘Hijab… Why?’ da sauransu.
Akwai littattafan da suka shafi kasuwanci da banki da da’awah. Haka kuma akwai littattafan Fikhu da Tawheedi da hadisai da tarihi da sauransu.