✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Bukaci Oshiomhole da ya sauka daga Mukaminsa

An bukaci Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adam Oshiomhole da ya sauka daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar domin ya kasa. Sanata Lawal Shu’aibu Mataimakin Shugaban…

An bukaci Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adam Oshiomhole da ya sauka daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar domin ya kasa.

Sanata Lawal Shu’aibu Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Shiyyar Arewa shi ne ya yi wannan kiran, ya ce hakika Oshiomhole ya kasa wajen gina jam’iyyar kamar yadda ya tarar da ita,

Jigon na APC ya kara da cewar maimakon jam’iyar ta kara samun tagomashi, sai koma baya take samu, a wata wasika daya aikewa Adam a ranar 27 ga watan mayun daya gabata, tana cewa wajibi ne ga shugaba a same shi da dattaku da kwarewa da kuma basira, domin gudanar da jagorancin al’umma. Wasikar mai taken abin takaici da kaito ga APC, Sanata Shu’aibu wanda ya fito daga Jihar Zamfara, inda jam’iyar ta yi mummunar asarar dukkan kujerunta ga Jam’iyar PDP,wanda hakan ya biyo bayan irin yadda shi Oshiomhole ya sa aka gudanar da zaben fidda ‘yan takara na mukamai dabam dabam a Jihar, bisa son ransa, ya kara da cewar tun lokaci mai tsawo akwai sabani akan ci gaban siyasar Jihar ta Zamfara, wanda shi Adam ya zama dan amshin shata ga Tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari.

Bayan wannan takaddama a tsakanin shugaban Jam’iyar da mataimakin nasa, akwai wata dambarwa kuma, a tsakanin Oshiomhole da Tsofaffin Gwamnonin Jihohin Imo Rochas Okorocha, Ibikunle Amosun na Jihar Ogun da kuma Tsohon Ministan Sadarwa Adebayo Shittu, duk akan zaben fidda ‘yan takara na Jam’iyar ta APC don shiga babban zaben kasa da aka gudanar, Adam Oshiomhole yayi gaban kansa wajen kin amincewa da ‘yan takarar da Rochas da Ibikunle suka tsayar, wanda hakan ya jawowa jam’iyar asarar rasa kujerun wadanan Jihohi, hazalika aka ki tsaida Adebayo Shittu domin ba shi da takardar shaidar yi wa kasa hidima.

Wannan kira da Shu’aibu yayi ga Shugaban jam’iyar, shi ne irinsa na farko da ya fito da ga bakin wani babban jigo a jam’iyar ta APC, wanda aka zabe su a rana 6 ga watan yunin 2018 a taron kasa da Jam’iyar ta yi.Bayan haka Mataimakin Shugaban Jam’iyar yace bai kamata a rinka gudanar da taron kwamitin gudnarwa na Jam’iyar a wajen Sakatariayar Jam’iyar ba, sannan ya zargi Adam da yanke hukuncin karshe a kana bin da kwamitin ne yake da hakkin yin hakan. Yace akwai ‘yan takara da yawa da Oshiomhole ya hana su tsayawa takara, ba tare da tuntubar kwamitin gudanarwa na Jam’iyar ba.

Mataimakin Shugaban Jam’iyar yace irin daraja da girmmawar da APC take samu daga magoya bayanta, duk yanzu babu shi, halayya maras kyau da nuna isa da ake yi wa ’ya’yan Jam’iyar da barazana ga manyan ’ya’yan Jam’iya irin su Gwamnoni da Sanatoci da sauran manyan jami’en Gwamnati,da shugaban yake yi ya sa sam Jam’iyar bata da wani tagomashi.

A cewarsa dangantaka tsakanin Jam’iya da Gwamnati na bukatar hadin kai domin samun nasarar aiwatar da tsare tsaren da aka tsara,bisa jadawalin Jam’iyar, amma ihu da bada umarni ga Jami’en gwamnati ta talabijin ko shafukan jarida, babu abin da zai kawo sai koma baya.

Ya ce “kada a yi min mummunar fahimta, ina fadin hakan ne a kan yadda Shugaban jam’iyya ke tafiyar da al’amuran jam’iyyar, ni ba ina neman kujerar shugabancin jam’iyyar ba ne, domin hakan ba zai taba yiwuwa ba, ko da na so don ni da Shugaban Kasa mun fito shiyya daya ta Arewa Maso Yamma, shawara ce don yadda ya kamata a gyara tsarin Jam’iyyar APC ta sake kasancewa kamar yadda ta ke, shugabanci idan an ba ka ka san ba za ka iya ba, sai ka sauka domin a samu ci gaban da ake bukata, don haka ina shawartar Oshiomole da ya koma gefe ya kyale jam’iyya ta bunkasa da kuma aiwatar da sababbin tsare-tsare da zai kai jam’iyyar ga cin ma gacci,”  a cewarsa.

Haka ma tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Sakkwato Malam Garba Nadama shi ma yayi irin wannan kiran na Shugaban Jam’iyar da ya sauka daga kan Mukamin nasa.