Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An ceto dalibai 40 wasu 8 sun rasu a rushewar makaranta a Legas – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce, dalibai takwas sun rasu yayin da aka ceto mutum 40 a makarantar firamaren Baden mai gini hawa uku da ta rufta a jiya Laraba da misalin karfe 10 na safe da ke unguwar Ita-Faji a Lagos Island, jihar Legas.

Jami’in hulda da jama’a na  hukumar NEMA a shiyyar Kudu maso Yamma Ibrahim Farinloye ne ya sanar da hakan.

ADVERTISEMENT

An kai dalibai 43 babban asibitin jihar Legas don yi masu jinya, a cikin wadanda suka rasu akwai wata mata mai juna biyu da wasu `yan biyu da ginin ya rufta da su.

ADVERTISEMENT