✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto masuntan da suka bace a ruwa bayan kwana 20

Wadansu matuka jirgin ruwa sun ceto masunta biyu ’yan kasar Costa Rika bayan kwana 20 da bacewarsu a cikin tekun kusa da kasar Jamaika. Wadanda…

Wadansu matuka jirgin ruwa sun ceto masunta biyu ’yan kasar Costa Rika bayan kwana 20 da bacewarsu a cikin tekun kusa da kasar Jamaika.

Wadanda aka ceton sun bayyana cewa, ceton da suka samu na da nasaba da albarkacin lokacin Kirsimeti.

Masuntan sun bace a tekun kusan makon uku kafin su samu agajin matuka jirigin ruwan da suke sufuri a tekun.

A cewar wani masanin yanayi da ke cikin matuka jirgin ruwan mai suna James Ban Fleet wanda ya mallaki jirgin Royal Caribbean, ya ce an ceto masuntan ne a tsakanin Tsibirin Grand Cayman na Birtaniya da Jamaika a daren Juma’ar makon jiya.

James ya ce, masuntan sun bar yankin Porto Limon na Kosta Rika sai barci ya kwashe su lokacin da suke zura rariyar kamun kifinsu a cikin ruwa, zura rariyar na daukar lokaci mai tsawo kafin su kammala. Suna cikin haka ne sai iska ta kwashe abin da suke zurawa a cikin ruwa, sai suka farka daga wannan lokacin sai suka yi batar hanya a cikin kwale-kwalensu.

Daga bisani sai man gas din kwale-kwalensu ya kare, sun yi kokarin komawa baya, amma hakan ya ci tura har suka kai tsawon kwana 20.

Masuntan sun bayyana wa wadanda suka ceto su cewa, suna da guzurin abincin mako guda da ruwa ne kadai, tun bayan mako dayan sai suka fara neman kifin da za su ci a matsayin abinci.

Mista James ya ce, “Daya daga masuntan ko tafiya ba zai iya yi ba, har sai da ma’aikatan jirgin ruwanmu suka taimaka wajen dauko shi a saka shi a cikin jirgin ruwan.”

Bayan ceto masuntan biyu, rukunin likitocin jirgin ruwan sun fara duba lafiyarsu kafin su fara ba su abinci da tufafi daga nan suka kai su asibiti. Ma`aikatan jirgin ruwan sun hada wa masunta tallafin kudi da ya kai Dalar Amurka 300 (kimanin Naira dubu 109 da 350.), don su sayi tufafi da abinci.

Mista James ya ce, wadanda aka ceto sun yi babbar nasara ganin yadda matuka jirgin ruwan da suka ceto su sun yi shirin doguwar tafiya mai nisa inda suka kwashe kilomita mai yawa daga kasar Kyuba a wannan lokaci.

Duk da yake jirgin ya canja shirinsa sanadiyar sauyin yanayin da aka samu, wannan ceto masuntan ba karamar sa’a suke da shi ba, da ace ba su da sa’a jirgin ruwan da ko kusa da su ba zai zo ba a wannan lokaci amma sai direbobin jirgin suka bi ta yankin Ocho Rios  a Jamaika bayan canja  shirinsu, hakan ya sa masuntan suka samu agajinsu.

Masuntar da aka kubutar sun ce, wannan nasarar kubutar da su da aka yi na da nasaba albarkacin lokacin Kirsimeti, wannan abin al`ajabi ne kasancewar su kwana 20 a teku suna neman agaji daga bisani kuma suka samu yanzu za su ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba.