Da Dumi Dumi

An ceto ‘yan gudun hijira 108 a tekun Libiya

An kubutar da ’yan gudun hijira 108 a gabar tekun garin Sabrata na Libiya.

Sanarwar da Ofishin Hulda da Kafafan Watsa Labarai na Rundunar Sojin Ruwan Libiya ya fitar ta ce an kubutar da ’yan gudun hijirar ne a nisan mil 18 a cikin tekun da ke Gabas da garin Sabrata mai nisan kilomita 78 daga Tarabulus Babban Birnin Kasar.

Sanarwar ta kara da cewa daga cikin mutanen akwai mata 17 da yara kanana 13.

Bayan an ba mutanen taimakon farko da suke bukata an mika su ga ofishin kula da shige-da-fice da ke Tarabulus.

Garin Sabrata dai ya kasance daya daga cikin manyan wuraren da bakin haure, galibi daga kasashen Afirka suke kaddamar da tafiya mai cike da hadari a cikin tekun Mediterranea, a kokarinsu na shiga Tarayyar Turai.

ADVERTISEMENT

Wani jami’in sojin ruwan Libiyan, Ayoub Gassim, ya ce an bai wa masu hijirar agajin gaggawa da magunguna; gabanin a dangana da su zuwa cibiyar tsare ’yan gudun hijira da ke yammacin garin Zawiyya.

Libya dai ta fada cikin rikici bayan tarzomar 2011 da ta yi awon gaba da gwamnatin Mu’ammar Gadhafi, sa’annan aka kashe shi. Kasar ta kuma zama mahadar bakin haure wadanda ke guje wa yake-yake da kuma bakin talauci a Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya zuwa Nahiyar Turai.

 

Share