✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci gaba da fasa rumbunan adana kayan abinci a Abuja

Gungun matasa sun dora daga inda suka tsaya a ranar Lahadi, inda suka ci gaba da nemo rumbunan da aka boye kayan tallafin COVID-19 a…

Gungun matasa sun dora daga inda suka tsaya a ranar Lahadi, inda suka ci gaba da nemo rumbunan da aka boye kayan tallafin COVID-19 a Abuja.

Majiyarmu ta rawaito cewa mutane da dama ciki har da matasa sun bude rumbun adana abinci da ke yankin Gwagwalada a Birnin Barayya, Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun ci gaba da kwasan kayan tallafi a rukunin masana’antu da ke Idu a Abuja.

A hangi mutane ciki har yara mata da maza suna dibar kayan tallafin da suka hada da shinkafa, taliya da sauran kayayyakin abinci.

A yanzu haka dai mutane na ci gaba da farautar rumbunan da aka boye kayan tallafin annobar COVID-19 a fadin Najeriya.