✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci tarar Jurgen Klopp fam 45,000

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta ci tarar kocin Liberpool, Jurgen Klopp Fam 45,000 kan kalaman da ya yi, sakamakon alkalancin da Kebin Friend ya…

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta ci tarar kocin Liberpool, Jurgen Klopp Fam 45,000 kan kalaman da ya yi, sakamakon alkalancin da Kebin Friend ya gudanar a gasar Firimiya.

Klopp ya soki yadda Friend ya gudanar da alkalancin wasan da suka tashi 1-1 da West Ham United, inda ya ce kwallon da suka ci tun farkon wasa halastacciya ce, amma aka hana.

Kocin ya ce, “Kwallon da muka zura a raga da aka ce  wai satar gida ce, ina da tabbacin cewa alkalin wasa ya san halastacciya ce.”

Hukumar ta tuhumi kocin da yin kalaman da suka shafi ingancin alkalin wasan da zarginsa da nuna fifiko.

Sadio Mane ne ya fara ci wa Liberpool kwallo tun kafin a je hutu, amma kuma James Milner ya yi satar gida a wasan da suka yi a ranar 4 ga watan Fabrairu.

West Ham ta farke ta hannun Michail Antonio tun kafin a je hutun rabin lokaci, sai dai Klopp ya kara da cewa tun daga nan ne Friend ya rike wasan sakamakon kuskuren da ya yi.