Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An ciro magogin hakori daga cikin wani bayan shekara 20

An ciro magogin hakori daga cikin wani bayan shekara 20

An ciro wani magogin hakora daga cikin wani da ya taba yunkurin hallaka kansa lokacin da yake tsare a gidan kurkuku.

An ciro magogin ne da ya hadiye bayan shekara 20, har ma an sake shi daga gidan na yari.

Koda aka ciro magogin da kyar da aka iya gane shi, saboda marikin ya riga ya zama baki, kuma asalin magogin ya narke.

Tsohon dan fursunan, mai suna Li ne ya je wajen likitoci bayan ya sha fama da ciwon ciki, wanda hakan ya sa aka tura shi wajen daukan hoton sassan jiki a birnin Schenzhen na kasar China, kuma hoton ya nuna cewa yana dauke da magogin baki a cikinsa.

Cike da mamakin abin da suka gani, likitocin sun tambaye shi yadda magogin ya shiga cikinsa, har ya makale a cikin hanjinsa. Daga bisa aka yi masa aiki, aka cire magogin.

Li, mai shekara 51 ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda ya ce ya hadiya magogin da niyyar ya hallaka kansa ne lokacin da yake zaman kurkuku.

Ya ce bayan kasancewarsa a kurkuku, ya kuma kamu da cutar kanjamau (HIB) ta hanyar tu’ammuli da miyagun kwayoyi, inda hakan ya sa ya ga abubuwa sun masa yawa, shi ne ya yi yunkurin hallaka kansa ya huta.

Amma abin mamaki shi ne yadda marikin magogin kawai baki ya yi, amma bai yi komai ba, sannan kuma Li ya karasa zamansa a gidan yari ya fito.

Daga baya ya daina shan kwayoyi, kuma ya samu sauki daga cutar ta kanjamau.