✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daga auren Zango da Suffy zuwa bayan Sallah

An daga auren fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango da Safiya Umar Chalawa (Suffy) zuwa bayan bikin karamar Sallah. Jarumi Zango ne ya sanar…

An daga auren fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango da Safiya Umar Chalawa (Suffy) zuwa bayan bikin karamar Sallah.

Jarumi Zango ne ya sanar da hakan a ranar Talatar da ta gabata a shafinsa na Instagram.

Jarumin bai sanar da dalilin daga ranar auren ba, amma ya bayyana cewa zai sanar da masoyansa sabuwar ranar aurensa idan har an sanya wata.

Ya ce, “Salam, ’yan uwa da abokan arziki. An daga ranar aurena zuwa bayan Sallah. Zan sanar da ku sabon lokacin da aka tsayar. Wadanda suka daura niyyar zuwa daurin aurena su dakata. Na gode Allah Ya bar zumunci da soyayya.”

Idan ba a manta ba dai tuni Zango ya kammala shirye-shirye don yin wannan aure, wanda da an yi shi ne zai zama karo na shida na jarumin ya yi aure tun daga na farko a shekarar 2006.

A katin gayyatar daurin auren da wakilin Aminiya ya samu an shirya daura auren ne da Masallacin Juma’a na Sarkin Gwandu da ke Jihar Kebbi a yau Juma’a da misalin 2:30 na rana.