Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An dage auren Zango da Suffy zuwa bayan Sallah

An dage auren fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango da Safiya Umar Chalawa (Suffy) zuwa bayan bikin Karamar Sallah.

Jarumi Zango ne ya sanar da haka a ranar Talatar da ta gabata a shafinsa na Instagram.

ADVERTISEMENT

Jarumin bai sanar da dalilin dage ranar auren ba, amma ya bayyana cewa zai sanar da masoyansa sabuwar ranar aurensa idan har an sanya.

Ya ce, “Salam, ’yan uwa da abokan arziki. An daga ranar aurena zuwa bayan Sallah. Zan sanar da ku sabon lokacin da aka tsayar. Wadanda suka daura niyyar zuwa daurin aurena su dakata. Na gode Allah Ya bar zumunci da soyayya.”

ADVERTISEMENT

Idan ba a manta ba dai tuni Zango ya kammala shirye-shirye don yin wannan aure, wanda da an yi shi ne zai zama karo na shida da jarumin ya yi aure tun daga na farko a shekarar 2006.

A katin gayyatar daurin auren da wakilin Aminiya ya samu an shirya daura auren ne a Masallacin Juma’a na Sarkin Gwandu da ke Jihar Kebbi a yau Juma’a da misalin 2:30 na rana.