✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage Balotelli daga wasanni uku a gasar Serie A

An dage Mario Balotelli, dan wasan gaba a kulob din AC Milan da ke Italiya har wasa uku bayan da alkalin wasa ya ba shi…

An dage Mario Balotelli, dan wasan gaba a kulob din AC Milan da ke Italiya har wasa uku bayan da alkalin wasa ya ba shi katin kora a wasan da kulob din ya yi da na Napoli a ranar Lahadin da ta wuce a gasar rukuni-rukuni ta Serie A.
Rahotanni sun tabbatar sau biyu alkalin wasan ya ba dan kwallon katin gargadi da hakan ta sa a karo na biyu ya hada masa da jan kati kamar yadda dokar kwallo ta tanada.
A wasan, kulob din Napoli ya doke na Milan ne da ci 2-1 da hakan bai yi wa dan wasan dadi ba.  Bayan an tashi daga wasan ne sai Balotelli ya nufi alkalin wasan inda ya rika antaya masa bakaken maganganu da hakan ta sa Hukumar kula da kwallo ta Italiya daukar matakin dage shi daga yin wasanni uku a gasar.
Da Balotelli bai tare alkalin wasan kuma ya zage shi ba, wasa daya kawai zai rasa amma saboda rashin da’ar da ya nuna ta sa hukumar dage shi tsawon wasanni uku.
Kenan dan kwallon ba zai buga wasan da kulob din Milan zai  yi da na Bologna da Sampdoria da kuma na Jubentus a gasar ba.
Balotelli ya samu nasarar zura kwallaye uku a cikin wasanani hudu da ya yi wa kulob din Milan a kakar wasa ta bana.
A wasansu da Napoli ne ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a karon farko a rayuwarsa amma daga bisani ya jefa kwallo daya a raga da hakan ta sa aka tashi wasan da ci 2-1.