✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage dan kwallo saboda rage yawan shekarunsa

Wani matashin dan kwallo a kasar Indiya Gourab Mukhi ya fuskanci fushin Hukumar Kwallon Kafa ta Indiya inda ta dage shi na tsawon wata shida…

Wani matashin dan kwallo a kasar Indiya Gourab Mukhi ya fuskanci fushin Hukumar Kwallon Kafa ta Indiya inda ta dage shi na tsawon wata shida saboda samunsa da laifin yin karya a shekarunsa na haihuwa.

Matashin mai shekara 28 ya ce shekarunsa 16 inda yake buga wa kulob din Jamshedpur da ke wasa a rukuni-rukuni na Indiya.

Asirinsa ya tonu ne bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Indiya (All India Football Federation) ta sanya sunansa a shafin yanar gizo a matsayin wanda ya kafa tarihi yana da shekara 16 kuma ya zura kwallo a gasar.  A tarihin gasar, ba a taba samun dan shekara 16 ya zura kwallo a gasar ba sai a kan Gourab.

Jim kadan da  watsa labarinsa a shafin yanar gizon ne wadansu da suka san matashin suka gabatar da koke inda suka nuna ainihin shekarunsa 28 ne ba 16 ba.

Hakan ya sa Hukumar  Kwallon Kafa ta Indiyar ta gudanar da bincike a Hukumar Rajistar Jama’a ta Kasar (Central Registration System) da Hukumar Gasar Rukuni-Rukuni ta Kasar, inda ta gano shekarun dan kwallon 28 ne ba 16 ba.

Hakan ya sa hukumar ta kafa kwamitin ladabtarwa kuma ta gayyaci dan kwallon don ya kare kansa.  Bayan ya kasa gabatar da shaidar shekarunsa 16 ne sai ta dauki matakin dage shi na tsawon wata 6.  Kuma ta soke duk kyaututtukan da ya samu a baya.

Kwamitin ya nemi kulob din Gourab Mukhi ya sake gabatar da sahihan bayanai kan dan kwallon da zarar ya kammala dagewar da aka yi masa muddin yana son ya ci gaba da yin kwallo a kasar.

Gourab Mukhi dai ya zura kwallo a ragar Bengaluru ne a gasar rukuni-rukuni ta Indiya a watan Oktoban da ya gabata.