Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An dage dan kwallon kwando saboda zargin yana dauke da juna-biyu

Rahotanni sun ce Hukumar Kwallon Kwando ta Amurka (FIBA) ta dage wani dan kwallon kwando mai suna Donell ‘D.J’ Cooper na tsawon shekara biyu bayan an yi masa gwaje-gwaje inda ake zargin yana dauke da juna biyu duk da kasancewarsa namiji.

Sakamakon binciken da hukumar ta yi a kan dan kwallon a bara ne ya nuna yana dauke da juna-biyu duk da kasancewarsanamiji.

ADVERTISEMENT

Donell ‘D.J’ Cooper dai yana yi wa Amurka wasa ne, kuma yanzu haka yana kokarin kulla kwantaragi da wani kulob din kwallon kwando a Bosniya sai dai hakan ba zai yiwu ba saboda dagewar da aka yi masa.

Kafar watsa labarai ta Eurohoops ta ruwaito cewa ana zargin  dan kwallon kwandon ya gabatar da fitsarin wata budurwarsa ce a lokacin da aka nemi a yi masa gwaji a bara. Kuma budurwar tasa  tana dauke da juna biyu ba tare da saninsa ba. Hankalinsa ya yi matukar tashi bayan an sanar da shi sakamakon gwajin da kuma dagewar shekara biyu ba tare da ya yi wasan kwallon kwando a ko’ina a duniya ba.

ADVERTISEMENT

Rahotannin sun ce ba ya ga dagewar Hukumar FIBA za ta ci shi tarar makudan kudi don ya zama darasi ga masu niyyar aikata irin haka nan gaba.