✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage dokar hana fita a Kaduna da sassauta dokar a wasu yankuna

A yanzu haka jama’ar Birnin Kaduna nada damar gudanar da harkokin kasuwancinsu kamar yadda suka saba yi ako wane lokaci bayan da gwamnnatin jihar ta…

A yanzu haka jama’ar Birnin Kaduna nada damar gudanar da harkokin kasuwancinsu kamar yadda suka saba yi ako wane lokaci bayan da gwamnnatin jihar ta dage dokar hana fita.

Mai taimakawa Gwamnan jihar akan harkokin watsa labarai Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a yau Talata, dokar hana fita ta dare da aka sanya ranar 31 ga watan Oktoba 2018 an dage ta daga yau.

Aruwan ya kara dacewa, an sassauta dokar a yankunan: Kujama, Kasuwan Magani da birnin Kaciya da ke jihar. Dokar a Kaciya zata fara daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe yayin da Kasuwan Magani da Kujama zata fara daga karfe 5 na yamma zuwa karfe 6 na safe.