Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An dage dokar-ta-baci a kasar Masar

An dage dokar-ta-baci a kasar Masar

Al’ummar Masar na maraba da dage dokar-ta-vaci a kasarGwamnatin kasar Masar ta bayar da sanarwar dage dokar-ta-baci a Talatar da ta gabata.

Tun daga ranar 14 ga Agustan da ya gabata ne sojoji suka kakaba wa kasar dokar-ta-baci da kuma hana yawon dare, tun bayan da suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Muhammad Morsi. Haka kuma sojojin sun yi nasarar dakile zanga-zangar nan ta zaman durshan, a lokacin.
Tun da farko, dokar-ta-bacin an tsara cire ta ne bayan wata daya, amma gwamnati ta kara wa’adinta da wata biyu a ranar 12 ga Satumbar da ya gabata.
dage dokar ya biyo bayan hukuncin kotun kasar ne, wanda ya tabbatar da cewa watanni biyu ne kadai gwamnatin ke da aikon karawa a matsayin dokar-ta-baci a kasar. Gwamnatin kasar, wacce sojoji ke ba kariya, tuni ta ce ta aminta da hukuncin kotun.
Kafin dage dokar-ta-bacin, hukumomin tsaro sun samu ikon kama mutane ba tare da waranti ba, kamar kuma yadda suke da ikon shiga gidajen mutane domin gudanar da bincike kai tsaye.
Da dama daga mutanen kasar sun dora alhakin durkushewar harkokin kasuwanci ga wannan dokar-ta-baci. Sun ce a lokacin ne ma ya kamata gwamnatin ta kirkiri hanyoyin samar da ayyukan yi ga ’yan kasa da bunkasa tattalin arziki.