✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage Gasar Copa America saboda cutar Kurona

Rahotannin da ke fitowa daga Kudancin Amurka sun ce  an dage Gasar Copa America da kasashen da ke Kudancin Amurka suke bugawa. Kamar yadda jadawalin…

Rahotannin da ke fitowa daga Kudancin Amurka sun ce  an dage Gasar Copa America da kasashen da ke Kudancin Amurka suke bugawa.

Kamar yadda jadawalin gasar ya nuna tunda farko, kasashe biyu ne za su hada gwiwa wajen daukar nauyinta a karon farko tun 1983. Kasashen sun hada da Ajantina da  Kolombiya.

Mahukuntan gasar sun ce ganin yadda cutar Kurona ta mamaye duniya musamman yankin Turai inda mafi yawa daga cikin ’yan kwallon da ke yin gasar suke kwallo a can irin su Lionel Messi na FC Barcelona da Neymar na PSG na Faransa da Luis Suarez na Barcelona da Marcelo na Real Madrid ya sa mahuhukuntan suka dauki wannan mataki.  Sannan akwai yiwuwar ba za a kammala kakar wasa ta bana a kan lokaci ba, ganin yadda kasashen Turai suka dage wasanninsu zuwa nan gaba.

Gasar da aka yi niyyar faratawa a ranar 11 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yulin bana, yanzu za ta gudana ne a shekara mai zuwa (2021) a tsakanin wadannan ranaku.