✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage gasar rukuni-rukuni a Masar

Saboda yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula a ’yan kwanakin nan a kasar Masar bayan hambarar da shugaban kasa Mohammed Mursi, Hukumar kula da kwallon…

Saboda yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula a ’yan kwanakin nan a kasar Masar bayan hambarar da shugaban kasa Mohammed Mursi, Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar a ranar Talatar da ta gabata ne ta bayar da sanarwar dage gasar-rukuni-rukunin kasar har sai illa masha’Allahu.
A ranar Talatar da ta wuce ne hukumar ta nemi hukumomin tsaro ta ba ta kariyar cigaba da gasar, amma hukumomin suka nuna hakan ba za ta yiwu ba.  Hakan ya tilasta wa hukumar dage gasar zuwa wani lokaci.
Kimanin shekara biyu kenan da kasar take dage gasar rukuni-rukunntai saboda matsalar tashe-tashen hankula.
A shekarar 2012 ne tarzomar da aka yi ta janyo asarar rayukan kimanin mutum 74 a filin wasa na Port Said da hakan ta sa aka dage harkokin kwallo na tsawon watanni 9.
Ga shi a wannan shekara ta 2013 kuma an sake dage gasar saboda matsalar tarzomar da ke gudana a kasar.
Sai dai dagewar ba ta shafi babbar kungiyar kwallon kafa ta Masar da ke hankoron zuwa gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Brazil a shekara mai zuwa ba.  Amma kungiyar za ta rika gudanar da wasanninta ne a filin wasan da ba za a bar ’yan kallo su shiga ba.